Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya nemi ya yi masa abokin takara a zaben Shugaban Kasa na 2007.
Tinubu ya nemi Atiku, wanda shi ne dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, da ya daina zubar wa da kansa mutunci ta hanyar furta kalamai na rashin gaskiya a yayin da Najeriya ke bukatar jagoranci nagari.
- WHO ta ayyana Kyandar Biri a matsayin larurar gaggawa ta duniya
- Zaben 2023: Jam’iyyu 14 da ke takarar Gwamnan Kano
Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi dangane da takarar musulmi da musulmi.
A wata hira ta musamman da ya yi da gidan talbijin na Arise TV ranar Juma’a, Atiku ya yi ikirarin cewa ya raba gari da tsohon gwamnan Jihar Legas ne saboda dagewarsa na zama abokin takararsa a zaben 2007.
A hirar tasa, Atiku ya ce takarar musulmi biyu a karkashin tikiti daya ne ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da Tinubu.
“Abin da ya janyo rashin jituwa tsakanina da Asiwaju [Tinubu] a siyasance tun 2007, ta faru ne saboda takarar Musulmi da Musulmi.
“Idan za a tuna cewa na fice daga PDP ne saboda tsarin karba-karba, sannan muka kafa jamiyyar ACN tare da Asiwaju.
“A wancan lokaci, Tinubu ya so ya zama abokin takara ta bayan na samu tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ACN a 2007, amma sai naki amincewa.
“Kuma a dalilin haka ne ya sauya sheka ya koma goyon bayan marigayi Umar Yar’adua wanda ya yi takara a jam’iyyar PDP. Saboda haka wannan shi ne dalilin da ya janyo rashin jituwarmu.
“Ban taba yarda da takarar musulmi da musulmi ba. Najeriya kasa ce mai kabilai da addinai daban-daban don haka ya kamata a ce akwai wakilci na addini a shugabanci, ” in ji shi.
Sai dai a wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, ya karyata ikirarin da Atikun ya yi, yana mai cewa Atikun ne da kansa ya nemi Tinubu ya yi masa abokin takara a 2007.
“Bari na fada karara kowa ya sani, Atiku ne da kansa ya nemi na yi masa takarar Mataimakin Shugaban Kasa a shekarar 2007. Kuma har a yanzu ina nan a kan addinin Islama, babu wani sauyi da aka samu.
“Ko a lokacin da kawo min tayin yin takara tare da shi [Atiku], ni Musulmi kuma ina da tabbacin ya san akida ta ta addini, in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, a farkon watan nan ne dai Tinubu ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na Shugaban Kasa.