✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya nemi Buhari ya janye kasafin kudin 2021 da ya gabatar

Ya kuma ce, kin bin shawarar da ya bayar zai zamto rashin kishin da ka iya jefa tattalin arzikin kasa cikin bala'i.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari, da ya janye kasafin kudin 2021 da ya gabatar wa ‘Yan Majalisar Tarayya, domin a cewarsa ya saba wa dokar kudirin kudin ta kasa.

Atiku ya kuma ce, Buhari ya sake yi wa kasafin kudin garan bawul yadda zai yi daidai da dokar kasafin kudin ta 2007 tare da la’akari da matsalolin tattalin arziki da kasa ta ke fuskanta.

Atiku, wanda ya yi takarar shugabancin kasar a jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya bayyana hakan ne a takardar da ya fitar a daren Juma’a.

Ya kuma ce, kin bin shawarar da ya bayar zai zamto rashin kishin da ka iya jefa tattalin arzikin kasa cikin bala’i.

“Gibin kasafin kudin naira tiriliyan 5.21 wanda yawan kudin ya zarce da kashi 3.5 cikin dari na adadin dukiyar da kasa ta samu a shekarar 2019.”

“Wannan ya sabawa dokar kudirin kudi ta 2007, wadda a bangare na 2, sashe na 12 sakin layi na 1 ta ce: yawan abubuwan da za a yi da kudi da kudaden da majalisa ta aminta a kashe a duk shekara bai kamata ya zarce yawan kudin shiga da za a samu ba da kuma rararsu.”

“Kada ya zarce kashi 3 na adadin dukiyar da kasa ta samu a kowace shekara,” inji shi.