✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya doke Tinubu a rumfar zaben Ahmad Lawan

Jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar zaben Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar zaben Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

A zaben shugaban kasa da aka fafata a rumfar zabe mai lamba 001B da ke Makarantar Firamaren Katuzu, Atiku ya samu gagarumar nasara da kuri’a 186 a yayin da dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu ya samu 107.

Dan takarar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu 41, Abiola na PRP ya samu 2 sai kuma Peter Obi na jam’iyyar LP da ya tsahi da kuri’a daya.

Idan za a iya tunawa Ahmad Lawan ya nemi takarar shugaban kasa a APC, amma ya fadi a zaben fidda gwani wanda Tinubu ya lashe.

Daga bisani ya dawo neman tazarce a wurinsa, inda aka yi ta takaddama da Bashir Machina, wanda a karshe Kotun Koli ta ayyana Lawan a mastayin halastaccen dan takara.