Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar adawa ta PDP, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zabe a Jihar Kaduna.
Atiku ya lashe zaben ne, duk da kasancewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dan a-mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Tinubu.
- An kwana ana rawa saboda faduwar Gwamna Darius zaben Sanata a Taraba
- Kwankwaso ya ci zaben shugaban kasa a Kano
Baturen zaben, Farfesa Muhammad Zayyan Umar, ya sanar da cewa Atiku ya yi nasara da kuri’u 554,360.
Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 399,293, LP ta zo na uku da kuri’u, sannan NNPP 92,962.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi nasara a 14 daga cikin kananan hukumomi 23 da ke Jihar Kaduna.
Jam’iyyar LP ta lashe kananan hukumomi bakwai a yayin da APC mai mulkin jihar ta ci kananan hukumomi biyu.
Alkaluma:
- Masu rajistar zabe – 4,335,208
- Mutanen da aka tantance – 1,418,046
- Kuri’un da aka kada – 1,401,376
- Kuri’u masu kyau – 1,360,153
- Lalatattun kuri’a – 41,223