✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Sun sa labule kwanaki kadan bayan kotu ta yi watsi da bukatar hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar siri da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

Tattaunawar tasu na zuwa ne kwanaki kadan bayan kotu ta yi watsi da karar da aka shigar na neman ta hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Atiku sun sa labule da Obasanjo ne a safiyar Asabar bayan ya ziyarci tsohon uban gidan nasa a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun.

Atiku shi ne wanda ya kasance mataimakin Shugaban Kasa a lokacin mulkin Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Sau hudu bayan nan Atiku yana tsayawa takarar zaben shugaban kasa amma ba tare ya kai bantensa ba.

A shekarar 2019 ya tsaya takara a jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a hannun shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari.

Kawo yanzu dai Atiku bai bayyana matsayarsa game da zaben 2023 da ke matsowa ba, duk da cewa ana rade-radin cewa zai sake fitowa a karo na biyar.