Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya shawarci Musulmi to sake kwato addinin musulunci daga masu tsatstsauran ra’ayi wadanda bala’in da suke haddasawa ya bata wa addinin suna.
Atiku wanda jigo ne a jam’iyyar APC ya bayar da shawarar ne jiya a sakon sallar da ya aike wa Musulmi kafin bikin babbar sallar da za a yi a gobe Juma’a.
Tsohon Mataimakin wanda ya yi fatan ’yan’uwansa Musulmi gudanar da bikin babbar sallahi lafiya ya ce kare musulunci shi ne babban kalubalen da Musulmi suke fuskanta a yau sakamakon balahirar da masu tsatstsauran ra’ayi ke haddasawa na rusa duk wata dabi’ar addinin dan’adam.
Ya yi takaicin yadda masu tsatstsauran ra’ayi suka rusa tattalin arzikin Arewa musamman ma Arewa maso Gabas tare da kawo cikas ga rayuwar al’ummar yankin.