✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku Abubakar ya kadu da labarin korar Moyes

Tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya kadu matuka a lokacin da ya samu labarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da…

Tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya kadu matuka a lokacin da ya samu labarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila ta kori kocinta Dabid Moyes a ranar Talatar da ta wuce.
Atiku Abubakar ya ce ya kadu ne musamman ganin cewa wasu daga cikin ’ya’yansa magoya bayan kulob din Manchestr United ne don haka ba su ji dadin wannan kora da aka yi wa kocin ba, yayin da wasu bangaren ’ya’yansa kuma suka yi murna da korar kocin.
“Wasu daga cikin ’ya’yana suna goyon bayan kulob din Manchester United. A yau wasu suna bakin cikin korar kocin yayin da wasu kuma suke murna, don haka na rasa bangaren da zan goya wa baya a ra’ayin ’ya’yan nawa. Abin da kawai zan iya cewa shi ne ina ba wadanda suke bakin ciki hakuri yayin da nake taya wadanda suke murna, yin murnar korar kocin”, inji Atiku Abubakar.