✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yau ASUU za ta yi taro kan shiga sabon yajin aiki

ASUU za ta yi zama kan yanke albashin lakcarori a yayin da gwamnati ke shirin biyan mambobin CONUA albashin wata takwas da ASUU ta yi…

A ranar Litinin ce Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) za ta yi taron gaggawa domin cim-ma matsaya kan sake tsunduma yajin aiki kan zaftare albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya mambobinta.

Majalisar Zartarwa (NEC) ta ASUU ta kira taron ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke shirin biyan albashin wata taskwas ga malaman jami’a da suka balle daga ASUU, wadda ta shafe wata takwas tana yajin aiki a baya.

Aminiya ta ruwaito wani jami’in ASUU da ya nemi a boye sunansa, yana cewa, “NEC din ASUU za ta yi zama a ranar Litinin 7 ga Nuwamba don cim-ma matsaya kan shiga sabon yajin aiki, saboda rabin albashin da aka biya mu a Oktoba.

“ASUU ta fusata da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi, don haka za ta yanke shawara a ranar 7 ga watan Nuwamba,” in ji shi ta wayar tarho a karshen mako.

Murna ta koma ciki

Kungiyar ta kira taron gaggawan ne kasa da wata guda bayan janye yajin aikin da ta yi wata takwas tana gudanarwa daga 14 ga Fabrairu zuwa 14 ga Oktoba, 2022.

Da yake magana game da zaman, wanda zai gudana a Jami’ar Abuja, wani dan kwamitin zartarwar ASUU ya ce yanke albashin ya fusata malaman jami’a kuma suna zargin Ministan Kwadago, Chris Ngige, ne ya sa aka yanke.

Za a biya malaman da suka balle daga ASUU

A yayin da ake wannan dambarwa, Gwamnatin Tarayya na shirin fara biyan malaman jami’a da suka balle daga ASUU suka kafa kungiyar CONUA, wadda ta tsame kanta daga yajin aikin na wata takwas.

Wani malamin jami’a kuma mamba a CONUA ya ce, “Mu ba mu shiga yajin aikin da aka yi a kwanakin baya ba.

“Mun rubuta wa Ministan Kwadago wasika kuma ya ba da umarnin a duba lamarinmu don a fara biyan mu,” inji shi.

Ya ce, Ministan Kwadago ya bai wa shugabanninsu tabbaci cewa ranar Litinin za a fara biyan su kudadensu, har da gibin da aka samu a albashin da aka biya su na watan Oktoba.

Hakarmu ta ji daga Shugaban CONUA na Kasa, Niyi Sunmonu, ta ci tura.

Amma kakakin Minista Ngige, Olajide Oshundun, ya shaida mana cewa za a fara biyan mambobin CONUA da ba su shiga yajin aikin na wata takwas ba.

Ba za mu biya wadanda ba su yi aiki ba —Ngige

A martaninsa ga ASUU, Ngige, ya ce zargin ba shi da tushe, babu wanda ya yanke wa lakcarorin ASUU albashi ko ya biya su rabi.

Ya kara da cewa an biya su ne na  iya kwanakin da suka yi aiki a watan Oktoba, domin babu wanda zai biya su ladar aikin da ba su yi ba.

Tun da farko Gwamnatin Tarayya ta tsaya kan bakanta cewa za ta aiwatar da tanadin Dokar Kwadago ta Kasa na rashin biyan ma’aikatan da suka yi yajin aiki.

Amma Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da yunkurin, tana mai kira ga gwamnati ta cika duk alkawuran da ta yi wa ASUU kafin su janye yajin aikin — ciki har da biyan hakkokinsu na albashi da kuma kyautata yanayin aikinsu.

Amma Ngige ya ce sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta kan yajin aikin kafin a san makomar albashin malaman jami’a na lokacin da ASUU ta shafe a cikin yajin aiki.