Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta yi watsi da tayin da aka yi mata na tallafin kudade domin ta janye yakin aikin da take ciki.
Shugabannin ASUU sun ki amincewa jama’a su yi karo-karon kudade domin biya wa kungiyar bukatun da suka sa ta shiga yajin aiki ne bayan an yi musu tayin hakan a safiyar ranar Asabar.
Hakan ya taso ne a lokacin da aka karbi bakuncin kungiyar a shahararren shirin Brekete Family wanda gidan rediyon Human Rights ke gabatarwa a Abuja.
Shirin ya gayyato Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke da jami’an kungiyar ne domin su yi wa ’yan Najeriya bayanin dalilin yajin aikin da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Gabanin haka, shahararren mai gabatar da shirin, Ahmed Isah, ya kafa asusun tara wa kungiyar kudade domin share mata hawaye ta janye yajin aiki.
A lokacin tattaunawar ta ranar Asabar, Ahmed Isah, ya gabatar da Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel, ya bayar domin sanyawa a asusun tallafin da aka bude a bankin TAJ.
Nuna kudaden a baiwar jama’a ke da wuya, shugaban kungiyar ya nesanta kungiyar da kudaden da ake tarawa.
A kan haka ne Ahmed Isah ya yi barazanar dakatar da gidauniyar tunda kungiyar ba ta bukata.
Yawancin da suka kira shirin ta waya dai sun bayyana furucin shiga na ASUU a matsayin rashin sanin ya kamata.