✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

ASUU ta tsawaita yajin aikin jami’o’in Najeriya da mako hudu

Daliban jami’o’i za su shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU), ta sanar da tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu.

Sanarwar da ASUU ta fitar a Litinin din nan na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke.

Hakan dai na zuwa ne bayan kammala wani zaman gaggawa na jiga-jigan kungiyar da ASSUn ta gudanar ranar Lahadi a Abuja.

Kungiyar Malaman Jami’ar ta kara da cewa, ta tsawaita yajin aikin ne da mako hudu, lura da cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta nuna wata alama ta kawo karshen zaman daliban a gida ba.

Kazalika, ASUU ta gode wa Kungiyar Kwadago ta NLC, da sauran kungiyoyin da suka mara mata baya wurin yin zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo karshen yajin aikin.

Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da Gwamnatin Tarayya, yanzu kuma gashi ta kara wata daya.

Idan har aka shafe wasu makonni hudu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin daliban jami’o’in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin Najeriya da gaza cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka kulla, ciki har da batun inganta rayuwar malaman da kuma dambarwar shigar da kungiyar tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi.