Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU), ta shiga yajin aikin da Kungiyar Kwadago (NLC) ta tsunduma a Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun ASUU Reshen Jihar Kaduna, Dokta Peter Adamu, ya sanar a ranar Litinin cewa ana umartar mambobin kungiyar su dakatar da ayyukansu.
- El-Rufai na neman Shugaban NLC ruwa a Jallo
- Taron gwamnonin PDP bata lokaci ne —APC
- Yadda yajin aikin NLC ya jefa Jihar Kaduna cikin duhu
- Gwamnonin PDP sun goyi bayan hana kiwon-sake
“Uwar Kungiya ta umarce ni daga ofishin shiyyar Kano, cewar dukkan mambobinta da ke Reshen Kaduna su shiga yajin aikin gargadi da aka fara.
“Ya kamata mambobi su san cewar ASUU wani sashe ne na kungiyar kwadago, don haka ya zama tilas a mara mata baya.
“Duk dan kungiyar da bai shiga yajin aikin ba, ya kwana da sanin cewa babu abin da ASUU za ta yi masa idan nan gaba gwamnati ta sako shi a gaba.
“Don haka dole mu hade kai don zama tsintsiya madaurinki daya,” inji Adamu.
Shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, ya ce matukar Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta biya bukatun ma’aikata ba, to tabbas yajin aikin zai dora daga kwanaki biyar da suka bayar na gargadi.
Daga cikin dalilan tsunduma yajin aikin, akwai korar ma’aikata 7,000 da Gwamnatin Jihar ta yi, tare da hana wasu ma’aikata 50,000 hakkokinsu tun daga shekarar 2017.
Tun bayan fara yajin aikin harkkoki da dama sun tsaya cik a Jihar.
Makarantu, filin jirgin sama, tashar jirgin kasa, wutar lantarki, ruwa, bankuna, asibitoci da sauransu duk an kulle su a ranar Litinin da yajin aikin ya kankama.