Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu a wasu jami’o’i biyu na Gwamnatin Jihar Kano.
Jami’o’in da lamarin ya shafa sun haɗa da Jami’ar Yusuf Maitama Sule YUMSUK da kuma Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil (ADUSTEC).
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar YUMSUK ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban ASUU reshen jami’ar, Kwamared Mansur Sa’id.
Sanarwar wadda kuma take dauke da sa hannun Sakataren ASUU reshen jami’ar, Kwamared Yusuf Ahmed Gwarzo, ta ce yajin aikin zai fara ne daga karfe 5:00 na Yammacin wannan Larabar, 29 ga watan Mayun 2024.
Aminiya ta ruwaito cewa, ASUU reshen jami’ar ta yanke wannan shawarar ce bayan zaman majalisar shugabanninta da ta gudanar a ranar Laraba, inda ta aike wa duk shugabannin sashen ilimi na jami’ar wasiku kan matakin da ta ɗauka.
A cikin wasiƙun, ASUU ta ba da umarnin dakatar da duk wasu harkokin karatu a jami’ar kama daga koyar da ɗalibai da sauran dangogin abin da ya shafi karantarwa da zaman kowane irin taro da ya danganci harkokin ilimi ko gudanarwa a jami’ar.
Shi ma a zantarwarsa da Freedom Radio, Dokta Aliyu Yusuf Ahmed, Shugaban ASUU reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, ya ce faɗi dalilin koken da suke yi wa Gwamnatin Kano.
A cewarsa, Gwamnatin ta gaza biyan malamai a jami’o’in biyu wasu hakkokinsu da suka rataya a wuyanta.
Dokta Ahmed ya bayyana koken yadda gwamnatin take fifita aiwatar da wasu ayyukan da ba su kai na sauke hakkin malaman muhimmanci ba.
Ya ce kuɗin da gwamnati ya kamata ta biya a matsayin haƙƙoƙin malamai a jami’o’in biyu da lamarin ya shafa ba su gaza naira miliyan 600 ba.
Ya buga misali da cewa wannan kuɗin da gwamnatin har yanzu ta gaza biyan malaman ba su kai rabin wanda za ta siya wa ’yan Majalisar Dokokin Kano motoci na alfarma ba.
Haka kuma, Dokta Aliyu ya yi zargin cewa akwai ragon azanci daga bangaren gwamnatin dangane da yadda ta fifita ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a wasu jami’o’in ƙasar Indiya, “ƙananan makarantu marasa daraja.”