Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wata uku.
Hakan dai ya biyo bayan kammala taron Kwamitin Zartarwa na Kasa na Kungiyar da ya gudana a Abuja ranar Lahadi.
- Wahalar man fetur ta sake kunno kai a Abuja
- Faston da ke karbar N310,000 ‘kudin shiga Aljannah’ ya gurfana a gaban kotu
’Yan sa’o’i dai kafin fara taron, ASUU ta yi harsashen yiwuwar tsawaita yajin aikin saboda abin da ta kira halin-ko-in-kula daga bangaren gwamnati.
An dai fara yajin aikin ne ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 da matakin gargadi na mako hudu, bayan gaza cim ma matsaya da Gwamnatin Tarayya.
Wasu daga cikin bukatun na ASUU sun hada da fitar da kudaden farfado da jami’o’i da yarjejeniyar kungiyar da Gwamnatin Tarayya ta 2009.
Sauran bukatun sun hada da kin biyan kudaden alawus-alawus na malaman da kuma tsarin biyan albashi na UTAS a madadin na IPPIS.
A lokacin da wa’adin ya kare, kungiyar ta tsawaita yajin aikin da mako takwas, kafin yanzu kuma ta sake kara wasu makonni 12 a kai.