Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta ayyana shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) saboda matsalolin da suka shafi jin daɗin ma’aikata waɗanda ba a warware su ba tsawon lokaci.
Yayin da yake magana ga manema labarai a ranar Laraba, Shugaban ASUU na reshen jami’ar, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya bayyana cewa yajin aikin ya zama dole saboda yanayin koyarwa da koyo a jami’ar da ke raguwa sosai.
- Muna yaƙar cin hanci daga tushe — Shugaban EFCC
- Tinubu ya kunyata waɗanda suka kyautata masa zato — Sarkin Yaƙin Yarbawa
Ya ce, ƙungiyar ta yi amfani da hanyoyi daban-daban tsawon lokaci don samar da mafita cikin lumana, amma babu wani sakamako mai kyau da aka samu.
“Daya daga cikin matsalolin shi ne rashin aiwatar da Yarjejeniyar Ayyuka (MoA) na 2021 tsakanin ASUU da gwamnatin jiha, wanda ya shafi ƙarin kuɗaɗen tallafi ga jami’ar da kuma rashin biyan kuɗaɗen alawus-alawus na Haƙƙin Aiki (EAA) da suka taru.
“Wani muhimmin ɓangare na Yarjejeniyar Ayyuka (MoA) na 2021 da gwamnati ta kasa cikawa shi ne bayar da Naira miliyan 50 a kowace shekara ga jami’ar.
“Kusan shekaru huɗu bayan amincewa da yarjejeniyar, gwamnatin jiha har yanzu ba ta biya ko kwabo ba a kan wannan lamari ba,” in ji Jauro.
Shugaban ASUU ya nuna damuwa game da rashin biyan kuɗaɗen EAA tsawon fiye da shekaru biyar, wanda ya jefa ma’aikata cikin matsaloli wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu duk da yanayin aiki marar kyau.
Dakta Jauro ya ƙara da cewa, duk da cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba hannu kan dokar albashi mafi ƙanƙanta na Naira dubu 30,000 a shekarar 2020, jami’ar har yanzu ta kasa aiwatar da wannan doka, inda ma’aikata ke ci gaba da karɓar albashin tsohon tsarin na 2012.
Ya kuma bayyana cewa akwai batun rashin biyan alawus na ƙarin girma tsawon shekaru huɗu da kuma rashin aiwatar da ƙarin albashi na kaso 35 da 25 cikin 100 ga ma’aikata masu koyarwa.
Ƙungiyar ta ce, gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar MoA ya tilasta musu shiga yajin aikin sai baba-ta-ganii ba tare da wani zaɓi ba.
Ya yi kira ga ɗalibai da iyaye da su fahimci matsayinsu, yana kuma neman su yi kira ga gwamnati ta cika alƙawuran da suka yi.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na farko da malaman jami’ar GSU ke shiga yajin aiki tun bayan kafuwar jami’ar shekaru 20 da suka gabata.
A wani yunƙuri na dakatar da yajin aikin, gwamnatin jihar ta amince da biyan Naira miliyan 265 a makon da ya gabata don biyan alawus na ƙarin girma.
Duk da haka, Dakta Jauro ya ce har yanzu ba su karɓi kuɗin ba, inda suka ce kawai sun karanta labarin amincewar ne a cikin jaridu.