Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta yi fatali da tsarin nan na Gwamnatin Tarayya da take yi wa duk wata kungiyar ma’aikata barazana da shi a lokacin da ta shiga yajin aiki.
NLC dai ta yi watsi da tsarin na ‘ba aiki ba biya’ da gwamnatin ke son yin amfani da shi a kan Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta shafe watanni takwas tana yajin aiki.
- Mutumin da ya sace injin hada Burodi ya shiga hannu
- Ayo Owodunni: Dan Najeriya ya zama Kansila a Canada
A baya-bayan nan ne dai ASUU ta janye tare da komawa bakin aiki bayan Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani.
NLC ta bukaci gwamnati ta cika dukkanin alkawuran da ta kulla da kungiyar ta ASUU gabanin komawa yajin aikin, ciki kuwa har da abin da ya shafi hakkokinsu na albashi da kuma kyautata aikinsu.
Hakan ne dai na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Shsugaban NLC, Ayuba Wabba tana mai bayyana cewa wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta saki dukkanin hakkokin malaman jami’ar a tsawon lokacin da suka dauka suna yajin aikin.
Wannan takardar dai ta fito ne bayan wani taro da Kwamitin Kolin Kungiyar ta NLC ya gudanar a Jihar Kebbi.
An shafe tsawon watanni 8 ana kai ruwa rana tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU dangane da yajin aikin gabanin cimma jituwa a makon jiya, wanda ya bayar da damar janye yajin aiki.
Sai dai Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya ce har sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta game da yajin aikin na ASUU ne tukuna za su samu tabbacin yiwuwar biyan malaman ko akasin haka.