Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, ya ce Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) za ta iya rasa rajistarta saboda rashin mika bayanan asusunta ga gwamnati sama da shekara hudu.
Ngige ya bayyana hakan ga manema labarai ne jim kadan bayan kammala taro da sabbin kungiyoyin nan na CONUA da NAMDA wadanda ke mazaunin kishiyoyin ASUU.
- An fasa idon amarya ana tsaka da shagalin bikinta a Kano
- Gwamnan Gombe ya nada sabbin Kantomomi a Kananan Hukumomin jihar 11
Ya ce gwamnati ta dauki matakin tsaro don bai wa CONUA kariya daga kowace irin barazana daga ASUU.
Ya kuma ce tsawon wadannan shekarun, kungiyar ta ASUU ta gaza mika bayanai kan yadda ta sarrafa kudaden mambobinta.
Ministan ya kammala yi wa CONUA da NAMDA rajista ta hanyar mika wa shugabanninsu muhimman takardun da suka dace.
Kana ya yi kira gare su da kada su bari a sake rufe jami’o’in kasar.
Ngige ya ba da umarnin CONUA da NAMDA su yi aikinsu gaba gadi ba tare da wani tsoro ba.
Yana mai cewa, gwamnati ta yanke shawarar rage wa ASUU karfi ne saboda barnar da ta haifar wa tsarin jami’o’in kasar nan.
Idan za a iya tunawa, a bara ne Gwamnatin ta kirkiri sabbin kungiyoyin sannan ta yi musu rajista lokacin da ASUU take tsaka da yajin aiki, domin ta rage mata karfi.