✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU: Fadar Shugaban Kasa ta kira malaman jami’a zaman sulhu

Kungiyoyin ma'aikatan jami'a za su halarci taron da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya kira

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya kira zaman sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma malamai da sauran ma’aikatan jami’a na Najeriya.

Gambari ya kira zaman ne bayan Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta tsawaita wa’adin yajin aikinta da wata uku bisa abin da ta kira gazawar gwamnati wajen biyan bukatun malaman jami’a da ta yi alkawari.

“Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne zai jagoranci zaman da zai gudana da misalin karfe 4.00 na yamma a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa,” inji sanarwar taron.

Malaman sun yanke shawarar yin hakan ne bayan cikar wa’adin wata biyu da suka kwashe suna yayin aiki da sunan bai wa gwamnatin isasshen lokaci ta gama nazare tare da yanke shawara kan bukatunsu.

Ganin sun shiga sabon yajin aikin ne Gambari ya kira zaman da za a gudanar a Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis da yamma, tare da ASUU.

Sauran mahalarta taron sun hada Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASUU) da sauran kungiyoyi kwararru da na kwadago masu rajista a jami’o’in da suka shiga yajin aikin da ya tsayar da harkokin karatu cik a jami’o’in gwamnati.

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai babu tabbaci daga kungiyoyin malamai da sauran ma’aikatan jami’ar game da halartar taron, wanda Ministan Kwadago, Chris Ngige, zai karbi bakunci.