Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani sabon kwamitin wanda zai sake nazari a kan yarjejeniyar da gwamnatin baya ta kulla da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU a shekarar 2009.
Sabon kwamitin mai dauke da mutum bakwai zai ba da shawara a kan hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalolin da su ke haifar da yajin aiki.
Ministan Ilimi Adamu Adamu wanda ya kaddamar da kwamitin, ya bukaci wakilansa da su dauki aikinsu da muhimmanci da kuma gaggauta kammala shi a cikin wata uku mai zuwa lura da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ke yi a yanzu.
A watan Fabarairun 2017 aka fara irin wannan tattaunawar tsakanin gwamnati da kungiyoyin ma’aikata daban-daban da ke cikin jami’oi, amma ba a cimma matsaya ba.
Ministan ya ce kwamitin zai yi nazari akan daftarin da gwamnati da kungiyar malaman jami’oi suka gabatar tare da jin ta bakin bangarori da dama na masu ruwa da tsaki a kan harkokin ilimi a fadin kasar.
Ana iya tuna cewa, a watan Fabrairun da ya gabata ne ASUU ta tsunduma yajin aiki na makonni hudu don yin gargadi ga Gwamnatin Tarayya kan wasu bukatunta da aka gaza biya mata.