Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da umarnin ci gaba da amfani da rigakafin COVID-19 na kamfanin Astrazebeca, duk da rashin tabbas da wasu kasashe ke da shi kan allurar.
Kwamitin kula da rigakafi na WHO ne ya ba sanarwar tare da cewa allurar na rage tasirin yaduwar cutar.
- COVID-19: Najeriya ta aminta da rigakafin AstraZeneca da kasashe 13 suka dakatar
- Majalisar Malamai ta nemi Ganduje ya cire wa Abduljabbar takunkumi
- Mutum 6 sun mutu, 54 sun jikkata a hadarin mota a Bauchi
- Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai
Kazalika, kwamitin ya ce allurar na ba da kariya ga wadanda aka yi musu ita da kuma wanda ya kusanci wanda aka yi wa rigakafin.
Sannan kwamitin, ya aminta da cewar allurar kamfanin ba ta da wata matsala, in kuwa aka samu sabanin haka, to da ma can wanda aka yi wa itan na da wata matsala ta daban.
Ko a cikin makon nan sai da wasu kasashe 13 ciki har da kasashen turai suka dakatar da amfani da rigakafin da kamfanin Astrazeneca ya samar.
Amma duk da haka Najeriya, ta aminta da allurar rigakafin, inda ta umarci mutanen kasar da su karbi allurar da yakini mai kyau.