Annobar COVID-19 ta sa asibitoci kin duba marasa lafiya saboda tsoron kamuwa da ita, abin da Gwamnatin Tarayya ta nuna fushi a kai.
Sakatare Gwamnatin Taryya, Boss Mustapha ya yi takaicin yadda hakan ke sanadiyyar mutuwar mutane a asibitocin.
Boss Mustapha ya ce gwamnati ta gano cewa asibitoci sun rage duba majinyata da ba cutar coronavirus ke damun su ba.
Shugaban na Kwamitin Ko-ta-kana na yaki da cutar ya ce abin kunya ne asibitocin koyarwa na gwamnatin tarayya su rika kin duba majinyata.
- An dage dokar hana Sallar Juma’a a Katsina
- Yadda gwamnati ke shirin bude makarantu a fadin Najeriya
- Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati
“Tsananin ya kai har cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya na kin karbar marasa lafiya saboda gudun kamuwa da COVID-19.
“Wannan abin takaici ne wanda ba za mu lamunta ba.
“An fi mayar da hankali ne kan COVID-19 saboda zamanta annoba a duniya. Idan ba a magance ta ba za ta iya halaka mutane da yawa,” inji shi.
Za a yi wa dokar kulle kwaskwarima.
Boss Mustapha ya ce kwamitin zai yi bitar matakan da aka sanya na hana yaduwar cutar nan da kwanaki biyu masu zuwa.
Baya nan kwamitin zai mika rahoto da shawarwarinsa ga shugaban kasa domin yanke hukunci.
“Yayin da muke bin matakan da suka dace, kwamitin na kira ga ‘yan Najeriya da su ba da muhimmanci ga yakin da ake da cutar.
“Kariya ce gare mu da iyalenmu da ma al’ummarmu.
“Muna bakin kokarinmu a yaki da cutar tare da dukkan masu ruwa da tsaki daga dukkan matakai a fadin Najeriya.
“Muma yin haka ne domin ganin an cimma matsaya tare da yin aiki bai daya da dukkan matakan gwamnati domin samun nasara.