✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asibitin Aminu Kano ya gudanar da aikin tiyatar laka na farko

An dai gudanar da aikin ne a kan wata mata mai kimanin shekara 53.

A karon farko a tarihi, Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano ya gudanar da aikin tiyatar laka a ranar Asabar.

Tabbacin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Darakta mai kula da Sahen Yada Labarai ta asibitin, Hauwa Muhammad Abdullahi, ta raba wa manema labarai a Kano.

Sanarwar ta ce babban likitan da ya jagoranci ayarin takwarorinsa wajen aikin, Dokta Musbahu Ahmed, ya ce an sami nasarar ne bayan asibitin ya samu kyautar na’urar da ake amfani da ita wajen aikin daga wani attajiri.

Ya ce an bayar da kyautar na’urar ne a bara, inda aka kafa ta a asibitin, yanzu kuma aka fara amfani da ita.

Ya yi bayanin cewa, “An kawo wani mara lafiya asibitin nan kimanin shekara daya da ta wuce zuwa sashen kula da laka, amma sakamakon rashin wannan na’urar, dole ta sa aka tura shi wani asibitin.

“Likitan ya kuma nuna godiyarsa ga Allah nasarar da ya ba su wajen gudanar da aikin,” inji sanarwar.

An dai gudanar da aikin ne a kan wata mata mai kimanin shekara 53, wacce ta zo daga Jihar Adamawa.