✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asensio ya kara wa Madrid tagomashi a teburin La Liga

Matashin dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid, Marco Asensio ya dawo wasa da kafar dama bayan ya kwashe tsawon shekara daya yana jinya. Kasa…

Matashin dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid, Marco Asensio ya dawo wasa da kafar dama bayan ya kwashe tsawon shekara daya yana jinya.

Kasa da minti daya da shigorwarsa ne dai, Asensio ya zura kwallo. Daga baya kuma ya taimaka aka jefa kwallo a wasan da Madrid din ta doke Valencia da ci 3-0 a ranar Alhamis.

Tun ranar 24 ga watan Yuli na shekarar 2019 ne dai Asensio ya samu rauni a kafarsa, da ya hana shi buga wasa har 29 ga watan Mayu wanda a lokacin ake hutun cutar coronavirus.

Nasarar da Madrid din ta samu ya sa ta matso kusa da kungiyar Barcelona a kan teburin La Liga da maki biyu.

A ranar Juma’a kuma Barcelona za ta fafata da kungiyar Sevilla inda hankula za su karkata ganin irin matsin lambar da Madrid take yi a kokarinta na daukar kambun gasar.