An kona gidaje da shaguna da wasu kadarori na miliyoin Naira a sabon rikicin al’ummomin Waja da Lunguda da ke Karamar Hukumar Lafiya-Lamurde a Jihar Adamawa.
Rikicin ya faro ne a almurun ranar Litinin inda wasu bata-bari suka rika cinna wa gidaje da shaguna wuta a garin Lafiya.
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ba a samu asarar rai rikicin ba, amma bata-garin sun kona gidaje hudu da shaguna 11.
A cewarsa, Kwamishinan rundunar, S.K. Akande, ya ziarci yankin da aka samu hasaniyar domin tabbaar da doka da oda a ranar.
A cewarsa, rundunar za ta sana kafar wando da duk wanda aka kama da alaka da tashin-tashinar.