Wani ƙazamin hari da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.
Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa.
Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.”
Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta tabbatar wa BBC cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu a harin ya kai mutum 51.
“Maharan sun shiga ne suka buɗe wuta ne kan mutane suna barci suka ji ruwan harsasai.
“Sun kashe mutane a gidaje da kuma kan titi, yanzu an ƙidaya gawarwaki 51, in ji Sunday Abdu, Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Filato.
Bayanai sun ce wasu mahara ɗauke da makamai ne suka yi harbin kan mai uwa da wabi a ƙauyukan Zike da Kimakpa, inda nan take mutane 47 suka mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata waɗanda aka kwantar da su a asibiti.
Wannan hari ya zo ne kwanaki 10 bayan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40 a yankin.
Dole a ɗauki mataki — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da ƙazamin harin, yana mai kira Gwamna Caleb Mutfwang da ya ɗauki matakin magance matsalar da ake samu.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Shugaban ya aike da saƙon jaje ga gwamnatin Jihar Filato da kuma jama’ar jihar, tare da kiran gwamnan jihar da ya ɗauki matakan da suka dace na siyasa wajen warware rikicin da kuma samar da dawwamammen zaman lafiya.
Yayin da yake bayani kan muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar, Tinubu ya buƙaci son juna da haɗin kai ba tare da nuna banbancin ƙabila ko kuma addini ba.
Shugaban ya buƙaci shugabannin addinai da na siaysa a ciki da wajen jihar da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen irin waɗannan hare hare da kuma ɗaukar fansar da ake gani, waɗanda ke jefa al’ummomi cikin tashin hankali.
Tinubu ya ce ya zama dole rikicin Filato da ya samo assali daga rashin fahimtar juna tsakanin kabilu da kuma addinai ya zo ƙarshe, yayin da ya ce ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike na haƙiƙa domin gano waɗanda ke ɗaukar alhakin rikicin domin gwamnatinsa ba za ta amince da hare-haren ramakon ba.
Baya ga hukunta waɗanda suke da hannu a rikicin, shugaban ya ce ya zama dole ga shugabannin siyasar jihar, a ƙarƙashin Gwamna Caleb Mutfwang da su magance assalin rikicin dake tsakanin jama’a.
Tinubu ya ce wannan rikici na tsakanin al’umma na sama da shekaru 20, kuma ba za a iya kaucewa dalilan da ke haifar da su ba, don haka ya zama wajibi a tinkare su ta hanyar adalci.
Cikin waɗanda aka kashe har da yara da tsofaffi — Amnesty
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Amnesty International ta yi kakkausan Allah wadai da kisan aƙalla mutum 51sakamakon harin ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Zikke.
Amnesty ta koka kan cewa da yawan waɗanda abin ya shafa sun kasa tserewa — ciki har da yara da tsofaffi — wanda sakamakon hakan ‘yan bindigar suka yi musu kisan gilla suka bar su cikin jini kace-kace.
“Dole ne a binciki gazawar hukumomi kuma a daina yi musu uzuri saboda yadda wasarere din da suke yi wa sha’anin tsaro ke haifar da waɗannan munanan hare-hare, makonni biyu bayan kashe mutum 52,” in ji Amnesty.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ɗin ta ƙara da cewa “yin Allah kawai da wadannan munanan hare-haren bai wadatar ba kuma dole ne a nuna jajircewar kare al’umma ta hanyar tabbatar da adalci.
“A yayin da Shugaba Tinubu ke ikirarin cewa gwamnatinsa tana sanya sabbin matakan tsaro don magance ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, hare-hare na bayan nan a jihar Filato na nuna cewa dukkan matakan tsaron da ake ɗauka ba sa aiki,” ta ce.
Ƙungiyar ta ba da alkaluma na yawan mutanen da aka kashe a Jihar Filato daga Disamban 2023 zuwa Fabrairun 2024, inda ta ce an kashe mutum 1,336.
Daga cikin wadanda aka kashe 533 mata ne sai yara 263, sannan maza manya 540.
Kazalika ta ce fiye da mutum 29,554 ne suka rasa matsugunansu, daga cikinsu 13,093 yara ne yayin da mata 16,461 suka rasa matsugunansu.