✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asalin yadda aka samo wakar Jaruma

Sunusi Hafeez, wanda aka fi sani da Sunusi Oscar 442 fitaccen darakta ne a masana’antar Kannywood. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana asalin fitacciyar wakar nan…

Sunusi Hafeez, wanda aka fi sani da Sunusi Oscar 442 fitaccen darakta ne a masana’antar Kannywood. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana asalin fitacciyar wakar nan ta Jaruma, da kuma yadda ya mayar da hankalinsa kan abubuwan da za su kawo wa Kannywood ci gaba musamman amfani da kafofin sadarwa na zamani.

Mene ne asalin wakar Jaruma?

Ita wakar Jaruma sai in ce wani irin abu ne da Allah Ya yi na cewa duk mutumin da ya yi hakuri, zai yi nasara a rayuwarsa. 

Wata rana ina aikin wani fim sai na kira mawakin na ce masa ina kusa da unguwarsu, sai ya zo ana sanyi lokacin ma ba zan manta wa. 

Na ce ga waka iri kaza. Na dauki kudi lokacin ma kudin bai taka kara ya karya ba na ba shi, ya karba ya ce zai yi.

Daga hagu Hamisu Breaker mawakin Jaruma sai Sanusi Oscar 442 wanda ya ba da umarni da kuma Mommee Gombe wadda ta hau bidiyon wakar

Waka ta dauki tsawon lokaci kusan shekara daya ba a yi ta ba. Daga wannan lokacin sanyin har zuwa wani sanyin kafin aka ba ni. Amma na ji dadin jin wakar lokacin da ya turo min. 

Amma abin da na shirya zan yi da ita ya riga ya wuce.

Sai na mayar masa da wakar ta Whatsapp sai na ce ya shirya wakar da shi za mu yi. Ka ga yadda lamarin yake.

Ana batun ka saya hakkin mallakar wakar Jaruma, yaya batun yake?

Ya kamata a rarrabe maka batun sayen hakkin malla da kake magana. Duk lokacin da ka kira mawaki ka ce masa ga waka kaza iri kaza da kake so wannan tsarinka ne, don haka za ku yi maganar tsada ka biya shi, ya je ya maka waka. Don haka, ba wakar mutum ba ce. 

Amma idan mutum ya je ya yi wakarsa, da basirarsa da tunaninsa wannan tashi ce. Sannan ka dauki nauyin bidiyo da kudinka, babu kudin wani a ciki, wannan mallakin ka ne. 

Sai dai a tsakninmu da mawaka muna da alaka mai kyau. Abunmu nasu ne, nasu namu ne.

Yanzu kusan ka fi mayar da hankali kan ba da umarnin wakoki, me ya sa haka?

Gaskiya na fi mayar da hankali kan bidiyon wakokin saboda idan ma ka yi fim din asara kake yi. 

Ni kaina ina da fim guda biyu a kasa, wadanda kudin kowane guda daya ya kai Naira miliyan biyu kuma ban san wanda zai saya ba zuwa yanzu. 

To ka ga bai kamata ka rika karbar kudin mutane kana lalata musu ba, kila dan jarin mutum ke nan. 

Tunda ka shiga ba ka fita ba, bai kamata ka sa wani a ciki ba. Wannan ya sa na dan tsagaita, ba wai barin fim din na yi ba.

Ganin yadda kake mayar da hankali kan wakoki, za ka bar fim ne?

Fim ba za mu bar ta ba. Kokarin da muke ta yi shi ne mu nemo wata hanyar dawo da martabar fim din mai dorewa yadda kowa zai amfana ba wai ni kadai ba.

Duk da mun samu gazawa wajen gwamnatin mai ci yanzu, ya kamata ’yan fim da suka yi gwamnatin su zauna da su, su taimake su, su kuma fada musu yadda za su taimaki masana’antar baki daya. 

Amma muna sa ran in sha Allah idan muka samu dama, mu za mu yi kokarin duk da za mu iya yi wajen dawo da martabar fim.

Darekta Sanusi Oscar 442

Za mu yi amfani da kwarewa da gogewa irin yadda kasashen da suka ci gaba a kan fim suka yi ake kallon fina-finansu, mu ma wannan hanyar za mu bi domin mu kai ga gaci.

Kana kokarin wajen fito da sabbin jarumai, mene sirrin?

Shi jarumi kadara ne wajen kowane darakta ko furodusa. Daga lokacin da darakta ya rasa jarumin da zai yi aiki, yana shiga cikin wani hali. 

Sau da yawa za ka ga fina-finanmu suna kama da juna saboda rashin wadatan jarumai. Mutum ya cancanta ko bai cancanta ba, haka za ka hakura ka sa shi saboda babu wasu. 

Saboda haka ne muke ta kokari wajen fito da sabbin jarumai maza da mata, wanda duk yake da sha’awar yin fim da su, zai kalla ya ga wane ne ya dace da labarinsa ya sa shi. 

Wannen ne burinmu. Idan babu jarumi, shi kan shi darakta bai da amfani.

A cikin wakokin da ka ba da umarni, wacce ka fi so, kuma me ya sa?

Wakar da na fi so a wajena, ita ce wakar da al’umma suka fi so. Duk wakar da mutane suke so, ni ma ina son wannan wakar. Wadda ma al’umma ba sa so sosai, ina sonta ni saboda ni na yi da hannuna. 

Kuma mutane suna son wakokin da na yi aikinsu da yawa, na cikin fim da wanda ma ba na fim ba, kamar na albam. Don haka ba zan ce maka ga kwaya daya tilo ba ina so, duka ina sonsu.

Duba da cewa Arewa ba a cika amfani da YouTube ba, kana ganin sakonninku za su rika isa ga mutane?

Lallai mutanen Arewa ba a damu da YouTube ba, amma sannu a hankali yanzu mutane sun fara mayar da hankali a kai. 

Yanzu za ka ga mutane sun hada talbijin dinsu da YouTube ne kai tsaye. Za ka ga babu DVD ma a gidan, idan ana bukatar wani abu, sai ka ga an nemo shi ne a YouTube sai  kalla talbijin din.

Ka ga an fara samun nasara. Dama komai a hankali ake farawa. Don haka muna sa ran hakan in sha Allah nan da lokaci kadan amfani da YouTube zai karade Arewa. 

Sannan kuma mu sake gyara sinima. Shi ma a koya wa mutane hanyoyin da ake kallon fim a sinima

Shin kana ganin YouTube zai samar wa mawaka kudaden da suka kashe har su ci riba?

A yanzu dai YouTube gaskiya ba zai iya rike dukkan mawaka da furudososhi da daraktoci da suke zuba kudadensu su yi fim ba.

Amma zai iya rikewa da a ce al’ummarmu ta Arewa za au koma YouTube din su rika kallon fim da muke yi don su. Ai muna da yawa a Arewa fiye da kowa a Najeirya. 

Mutanen da suke Hausa a nan Arewa da Kudu suna da yawan da sun ishe mu. Da za ayi haka, da ba mu da wata damuwa ko takaici, sun ishe mu amfana.

Ba ma waka ba kawai ba, har fim din ma da mutanenmu za su koma su rika kallon abun da muke yi, da za mu samu amfani sosai. Za mu yi duk abin da ya kamata, mu sake yin wani ma wanda ya fi wanda muka yi idan muna samun riba. 

Da ma abun da ya sa aka samu matsalar tun farko shi ne shi kansa sakon da ake kaiwa na DVD a wancan lokacin ba ya zuwa wasu wuraren ko kauyuka.

Amma yanzu ga abin nan a hannunka wayarka, za ka shiga ka kalla ba ruwanka da wanda zai sayar maka da mai kyau ko mara kyau. 

Ka ga da al’ummanmu za su gane hakan, da duk mawaki ko dan fim zai ji dadi.

Lura da yanayin ci gaba da ake samu a duniyar fim musamman ta hanyar amfani da kafofin zamani, yaya kake kallon Kannywood nan zuwa wasu shekaru masu zuwa?

Ita masana’antarmu ta sha bamban da sauran masana’antun fim na duniya, domin su sun yarda da fim a wajensu abu ne na ci gaba. Kuma duk mutumin da yake son ci gaba a duniya, zai rika kirkire-kirkire da kawo abubuwa sababbi wadanda al’ummarsa ba za su gaji da kallonsu ba. 

Amma mu a masana’antarmu an tara mutane ne makiyan juna, duk wani ci gaba da zai zo wa masana’antar, mutum shi kadai ne zai je ya rufe kansa a daki ya samu.

Idan a wajen gwamnati ne ko wani, haka zai je ya yi shi kadai ba zai dauki wani ba su je tare. 

Wasu irin mutane ne Allah Ya sa a masana’antar wadanda ba sa son masa’antar ta ci gaba. Kadan ne daga ciki suke da imanin taimakon na kasa da su.

Wane kira kake da shi zuwa ga masu ruwa da tsaki a Kannywood kan cin moriyar YouTube da sauran fasarar zamani?

Kira ga masu amfani da YouTube shi ne su kyautata YouTube dinsu da kyawawan kaya wadanda al’umma za su rika kalllo suna nishadantuwa suna jin dadi. 

Kada mu dauki YouTube kamar wani dama da aka taba yi na DSTV a wani lokaci can inda suke neman fim, mutane suka rika yin fim a kwana daya suna kaiwa domin su rika samun kudi.

Dalilin wannan inna- rududu na yadda aka rika yin fim marasa kyau, ya sa su kansu tashar ta African Magic suka raina mu. Suka ga cewa ba mu san abin da muke yi ba. 

Kuma mafi yawan wadanda suka rika kai fim kansu suka sani kawai babu tsari mai kyau. 

Da za a bi a hankali da kowa zai amfana, har na kasa ma su zo su amfana domin abun zai dore.

Wane kika kake da shi zuwa ga masu kallo?

Masu kallo su rika hakuri da mu. Duk abun da suka gani da bai dace, su rika fada mana ta hanyar da ta dace. 

Kada su yi fushi ko su shiga kafofin sadarwa suna zagi. Su gane cewa mu ma mutane ne, muna da hagu da dama, za mu iya yin daidai za mu yin ba daidai ba. 

Don haka duk wanda ya ga mun yi kuskure, idan masoyi ne na gaskya, zai sanar da kai cewa kaza da ka yi ba daidai ba ne. 

Ko ba komai mu Musulmai ne, kuma muna sa ran za mu cika da imani, kuma babu Musulmi da zai so kada wani Musulmi ya cika da imani. 

Don haka a ci gaba da hakuri da mu. Idan an ga kuskure a fada mana.