Binciken gano diddigin tarihin mutane wata matsala ce mai cin rayuwar masu bincike da waɗanda ake yi wa binciken. A lokacin da ilimi ya bunƙasa, kowace al’umma ƙoƙari take ta taskance tarihin asalinta.
Wurin da gizo ke saƙa shi ne, babu mai nunin gidansu da hannun hagu. Maimakon a yi canjaras ga abu guda, sai a ga kowane bakin wuta da irin nasa hayaƙin. A ƙarshe, a kasa rarrabe tatsuniya da tarihi da tarihihi da ƙari-faɗi da kintaci-faɗi da jita-jita hadisin Bamaguje.
Ƙudirin wannan bayani ko bincike ba suka ba ne, ko kushe ga ƙwazon magabata a kan asalin Bahaushe da harshensa. Ganin cewa, abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa ake son a sake farfaɗo da matakan al’ada na tantance tarihi da bibiyar diddigin asalinsa.
Asalin asali a al’ada
Asali, kalmar Larabci ce, gangariyar Hausa ita ce “tushe” ko “dugi.” A al’adar mutanen duniya, a tsarin ƙabilu, akwai manya da ƙanana. A siyasar zamaninmu, akwai masarauta da talakawa. A tattalin arziki, akwai mawadata da kuma moro (talaka). A addini, akwai masu bi akwai makangara. A wayewa, akwai ƙauyawa akwai ’yan birni. A sani, kuma akwai malamai ’akwai jahilai. A ɗiyauci, akwai ’yantattu akwai bayi. Bugu-da-ƙari hatta a zaman gari, akwai ’yan gida akwai baƙi. Inda matsalar take a al’adance babu mai yarda ya ce, asalinsa na da cikas. Shin wace ƙabila za ta yarda a ce da ita ƙarama? Wa ke son a danganta shi da talauci? Wa zai yarda da cewa matsiyaci ne tushensa? A addinance, wa zai so a kira kakanninsa makangara ne? Ko ɗan kauye. A ko yaushe dan Adam ya ƙi jinin a ce shi jahili ne. Da an ce wa mutum bawa, za a ga fushinsa bayyane. An san da cewa mai rai baƙon duniya ne, idan mutum ya yi kaka-gida a wuri ba ya son a kira shi baƙo mai suna tafaffe a ma’aunin ’yan gida zaunannu.
Waɗannan abubuwan da makamantansu ya kyautu masu nazarin kowace al’umma su kiyaye su. Tilas waɗannan abubuwa su yi naso ga rubutun mai rubutu a kan tushen al’ummarsa ko ta wasu. Idan al’ummarsa ce, zai kasance magori wasa kanka-da-kanka. Idan ko kan wata al’umma ce daban yake rubutu, dangantakarsa da ita na iya shiga cikin rubutunsa sosai. Matsalolin da ake fuskanta a Afirka su ne, ba a samu tattara tarihinmu a rubuce ba. Ta fuskar adabinmu waɗanda ba su ko sansu ba. su ke fashin baƙinta wajen tantance tarihinmu. Kai! Hatta Turawa da ’yan barandarsu.
Don haka duk wanda zai yi bincike a kan tushen wata al’umma, ya kyautu a san: A ina ya samo kayan aiki. Yaya ya sarrafa su? Wace dangantaka yake da ita da al’ummar? Shin ɗan ƙabilar ce? A’a maƙwabcinta ne? Koko baƙon haure ne? Me ya motsar da shi ya shiga ɗawainiyar rubuta tarihin? A kan waɗanne tussan asali ya baje kolinsa na fede zaren tarihin.
A al’adar asalin asali, kowane ɗan zuriya so yake ya rufe duk wata tangarɗa ga tarihinsa. Yana son ya danganta zuriyarsa da ɗaukaka da ƙwazo da basira da daraja ta musamman. Idan magabcinsa zai yi bincike a kansa da wuya ya yi masa adalci. Idan masoyinsa ne da wuya ya fallasa shi. Mai ƙoƙarin binciken asalin asali na wasu ko nasa, sai ya sanya masu karatun aikinsa cikin ƙunci da dawara na ina gaskiya take? Wannan ya tilasta a dubi karin maganar nan na ‘Kare duk sanda ya yi cizo da gashinsa ake magani’. A nazarci hujjojin raba-gardama a zuba su gadon adabi dole, a fayyace gefen da salka ke tsiyaya. Irin wannan halin tarihin asalin Hausawa ya shiga. Domin fatan haka ta cimma ruwa sosai, ga yadda ya kamata tsarin salon tafiyar nazari:
Wane ne Bahaushe?
Na tabbatar ƙasar Hausa ta riga Bahaushe zama a sararin duniya, amma duk da haka da ba Bahaushe ya fara sauka a kanta ba da ƙasar wasu ce ta daban. Bahaushe dole ya kasance a wajen iyaye uba da kaka duk Hausawa ne. A same shi yana bugun ƙirjin zama Bahaushe mai iƙirari ko alfahari da wata zuriya daga cikin zuriyar Hausawa. Samunsa cikin ƙasar Hausa ba tilas ba ne, kamar yadda addini da sana’a ba su cikin shika-shikan tantance shi. A ganin masana irin su John Paden da Abner Cohen sun yarda da miƙa wuya ga tantancewar Barkow:
“Ƙoƙarin tantance zaman mutum Bahaushe ya danganci cuɗanyarsa da walwalarsa cikin abokan sabga. Kalmar Hausa ta ƙunshi taron dangi na sassan ƙabilu barkatai.”
A maganar Mahadi Adamu, Bahaushe shi ne:
“Wanda a tarihinsa daga ƙasar Hausa ya tsira ko zuriyarsa ta fuskar iyaye maza, haka kuma waɗanda suka shaƙu da al’adun Hausawa sosai suka riƙe harshen da ɗabi’unsu da addininsu. Duk da haka, tilas a ba da kafa ga Fulani da suke zaune a ƙasar Hausa.”
Cikin yunƙurin tantance Bahaushe ya kyautu a waiwayi ƙirar zatinsa da ɗabi’unsa, domin fayyace Bahaushen gado da ka-zo-na-zo da maziyarta da maƙwabtan da aka Hausantar a ilimance. Bahaushen asali za a same shi:
“Yana da baƙi sosai irin na jama’ar tsakiyar Sudaniyya. Zubin kansa na da tsawo da ƙurungun kai mai ɗan jemo, za a same shi…”
Waɗannan siffofi na zati da launi, idan aka ƙura musu idon nazari za a iya fitar da Bahaushe kai-tsaye a taron jama’a da ke zaune a kasarsa. Turawa da suka ɗan zauni Bahaushe bisa yaudara suka karanci halayensa suna cewa:
“A ɗabi’a ya ɗara Bafulatani tsage gaskiya da rashin yarda. Mutum ne mai kunya, kuma yana da nagartattun ɗabi’u fiye da Bayarbe.”
Bayan samun wannan ɗan hasken ya kyautu a ɗan waiwayi ma’anar harshensa domin a gwama su a fitar da madaidaiciyar fahimta.
Ya kira ƙabilarsu da sunan. A wani Zubin su kira fasahar da suke da ita da sunan.
Manazarta Hausa a wajen ƙasar Hausa suna bai wa kalmar ‘Hausa’ ma’anoni mabambanta. Wadansu daga cikinsu su suka haifar da ruɗani da ake ciki a yau. Masana irin su Willis, suna ganin da harshen Hausa da na Bantu duk harsunan gamin-gambiza ne. A ganinsu, harshe da addini da al’ada dole a sa su cikin bayanin harshen. M. G. Smith, na da ra’ayin kalmar ‘Hausa’ ita ce harshen. “Polly Hill” ya mara masa baya da ƙara cewa, ba ƙabila ba ce bare zuriya, wanda duk aka haifa da harshen shi ne. Tunanin Guy Nicholas, ya ɗan fi faɗi, domin ya hangi kalmar ‘Hausa’ a matsayin wata muhimmiyar ƙabila a Afirka, yana da fahimtar ba dukkan masu magana da Hausa ne Hausawa ba. Abnar Cohen, ya aminta da zaman kalmar ‘Hausa’ ƙabila. Jeromo Barkow, ya haɗa biyu cewa, harshe ne kuma wata wayewar kan zamani ce. Wadannan ka-ce-na-ce duk ba su gusar da Hausa ga zama harshen Hausawa ba, wanda ba Bahaushe ba da ke Hausa aro ya yi, in aron ya yi tsawo ya rikiɗa ya koma Bahaushe.
Mece ce Hausa?
A nan ma, masana ba su yi ƙamfar fito da ra’ayoyinsu ba, domin lalubo tabbatacciyar ma’anar harshen Hausa ba. A wata fassara su kira ƙabilarsu da sunan. A wani zubin su kira fasaharsu da suke da ita da sunan. A fagen yaƙi, wadansu kan kira ƙasar Hausa da ke hannun Fulani ‘Hausa’ ga su nan dai. Manazarta Hausa a wajen ƙasar Hausa suna bai wa kalmar ‘Hausa’ ma’anoni mabambanta. Wadansu daga cikinsu su suka haifar da ruɗanin da ake ciki a yau. Masana irin su Willis, suna ganin da harshen Hausa da na Bantu duk harsunan gamin gambiza ne. M.G Smith, na da ra’ayin kalmar ‘Hausa’ ita ce harshen. Polly Hill ya mara masa baya da ƙara cewa, ba ƙabila ba ce ko zuriya, wanda duk aka haifa da harshen shi ne. Tunanin Guy Nicholas ya ɗan fi faɗi, domin ya hangi kalmar ‘Hausa’ a matsayin wata muhimmiyar ƙabila a Afrika, yana da fahimtar ba dukkanin masu magana da Hausa ne Hausawa ba. Abner Cohen ya aminta da zaman kalmar ‘Hausa’ ƙabila. Jerome Barkow ya haɗa biyu cewa, harshe ne kuma wata wayewar kan zamani ce. Frank Salmone ya hangi haɗarin da ke cikin fassara kalmar ‘Hausa’ da al’ada.
Matsayin Harshen Hausa a cikin Afirka
Wannan wata dama ce za mu rairaye ra’ayoyin da ke kwatanta Hausa da Bantu, da kuma masu ganin Hausa ba ta da wani tarihin asali da ma za ta tsaya a yi nazari. Haka kuma, za mu gano tsawo da faɗin harshen Hausa a duniyar da Bahaushe ya zauna da waɗanda suka yi tarayya a yaƙin neman jama’a da su da waɗanda ya cinye da waɗanda suka shige masa hanci ya kasa fyacewa. A cikin shimfiɗar Littafin ”The Northern Tribes of Nigeria” marubutan sun ce:
“Yanzu bari mu fara gabatar da mutanen da suka fi kowa bazuwa a arewacin Najeriya, Hausawa.”
A hasashen Williams F. S. Miles, ya kalli Hausawa da cewa:
“Miliyan ashirin na tsayayyun mutane zaunannu musamman a Arewacin Nijeriya da Nijar su ne Hausawa. Hausawa sun fi kowace ƙabila yawa a Afirka ta Yamma.”
Fitaccen masani ilimin harsunan duniya Russell G.Schuh ya faɗaɗa hasashen takwarorinsa da cewa:
“Babu saɓani ga kasancewar Hausa ɗaya daga cikin manyan harsunan duniya. Bayan Larabci, ta fi kowane harshe yawan (masu magana da shi a matsayin harshensu) a ƙasashen Afirka.”
A ma’aunin Royal Scottish Museum, ga irin nauyin harshen Hausa da Hausawa a wajensu:
“Hausawa su ne mafi yawan ƙabila, kuma mafi yawan bazuwa a Afirka. Akwai Hausawa da waɗanda Hausa ta rikiɗe (Hausantar) a manyan birane na Afirka ta Yamma da Afirka ta Arewa. Mafi yawansu (Hausawa) sun mamaye Arewa-maso Gabashin Jamhuriyar Nijar da Benuwai.”
Babu wai, al’ummar da ta samu wannan shaidar tana kasancewa kan takarda a ƙididdirgar al’ummomin Afirka da duniya ba a yi musu adalci ba idan aka ƙi zama a tantance asalinsu. A harsunan duniya, Hausa ba ƙyalle ba ce, ko cikin gida Afirka. Mamaye duniyar Afirka da Hausawa suka yi da masu magana da harshen Hausa suka yi, shi ya zama wata allura ta zaburar da mu tono ruwa domin Hausawa sun ce, yana ƙasa sai ga wanda bai tona ba.
Daga Bishir Ɗanƙaura
Za mu ci gaba a mako mai zuwa in Allah Ya so