✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arteta ba zai jagoranci wasan Arsenal da City ba saboda Coronavirus

Arteta ya taba kamuwa da cutar a watan Maris na 2020.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ba zai jagoranci ’yan wasan kungiyar ba a wasan Firimiyar Ingila da za su fafata da Manchester City a ranar 1 ga watan Janairu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus da ya yi a karo na biyu.

Sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Laraba ta ce, “Mikel Arteta bai zai jagoranci ’yan wasanmu ba a karawar da za mu yi da Manchester City a ranar sabuwar shekara bayan gwaji ya nuna cewa ya kamu da cutar Coronavirus.”

“Mikel yana killace kamar yadda ka’idodin mahukunta suka tanadar kuma muna yi masa fatan alheri,” a cewar sanarwar Arsenal.

Bayanai sun ce mataimakansa Albert Stuivenberg da Steve Round ne za su jagoranci ’yan wasan kungiyar yayin da za su karbi bakuncin Ciyu a filin wasa na Emirates.

Wasu daga cikin ’yan wasan irinsu Calum Chambers, Cedric Soares, Takehiro Tomiyasu da Ainsley Maitland-Niles ba su buga wasan da Arsenal doke Norwich da ci 5-0 a ranar 26 ga Disamba ba bayan sun kamu da cutar.

Ana iya tuna cewa Arteta ya taba kamuwa da cutar a watan Maris na 2020.