Arsenal na fatan sayen ɗan ƙwallon Brentford, Christian Norgaard, da zai maye gurbin Thomas Partey.
Wasu majiya na cewa farashin da Arsenal za ta ɗauki ɗan wasan na tawagar Denmark mai shekara 31, zai kai £10m da karin £5m idan ya taka rawar gani da karin tsarabe-tsarabe.
- Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump
- ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna
Arsenal ta daɗe tana zawarcin Norgaard, wanda tanzu take fatan zai maye gurbin ɗan kasar Ghana, mai shekara 32, wanda bai amince da ƙunshin yarjejeniyar da Arsenal ta gabatar masa, domin ya ci gaba da taka mata leda.
Kwantaragin Partey za ta kare a mako mai zuwa, idan kuma ba a kai ga cimma wata yarjejeniya ba, zai bar Gunners.
Norgaard, wanda yake da sauran yarjejeniya da Brentford zuwa 2027 ya koma ƙungiyar a 2019 daga nan ya zama kashin baya a karkashin Thomas Frank, wanda ya koma horar da Tottenham.