✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal za ta sayi Ndidi kan Naira Biliyan 18.6

Rahotannin da ke fitowa daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila sun ce kungiyar ta shirya tsaf don ta sayi dan kwallon Najeriya…

Rahotannin da ke fitowa daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila sun ce kungiyar ta shirya tsaf don ta sayi dan kwallon Najeriya Wilfred Ndidi da ke buga kwallo a kulob din Leicester City kan Fam miliyan 40 (kimanin Naira biliyan 18 da miliyan 650).

Arsenal ta ce za ta yi haka ne da zarar an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a wata mai zuwa.

Kungiyar Arsenal ta ce tana sa ran za su yi musayar ’yan kwallon biyu ne da dan kwallonsu Granit Dhaka da Wilfred Ndidi inda za ta cika Fam miliyan 40 wajen dauko Ndidi daga Leicester City.

Sabon kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce zai yi musayar ce saboda ya karfafa ’yan kwallon tsakiyarsa ganin an fi samun matsala daga bangaren tsakiya.

Idan za a tuna a makon jiya ne kulob din ya nada Arteta, tsohon dan kwalon kulob din a matsayin sabon koci saboda kalubalen da kulob din ke fuskanta a kakar bana.

Mikel Arteta shi ne Mataimakin Kocin kulob din Man City amma yanzu ya zama  kocin Arsenal.

Ndidi yana daga cikin ’yan kwallon da tauraruwarsu ke haskakawa a gasar Premier ta bana wanda hakan ya sa kulob da dama ke rububi a kansa da suka hada  da kulob din Arsenal.