Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala cinikin daukar dan wasan tsakiya na kasar Ukraine, Oleksandr Zinchenko, daga Manchester City.
Zinchenko wanda ya buga wasanni da dama a bangaren hagu na bayan Man City, wasa 15 kawai ya buga a kakar wasan da ta gabata a yunkurin kungiyar na kare kambun Firimiyar Ingila da ta dauka.
- Mene ne bambancin ’yan siyasa da ’yan ta’adda?
- An kama matashin da ya yi wa kanwarsa fyade sau 2 a Gombe
Dan kwallon mai shekara 25 ya je Arsenal ne daga zagayen da City ke yi a Amurka don kammala komawarsa tasa bayan Arsenal ta amince da yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 30.
Ya zuwa yanzu dai shi ne dan wasa na biyu da yake komawa Arsenal daga City a bazarar nan.
Tuni Gabriel Jesus ya koma Emirates kan fan miliyan 45, inda har ma ya ci mata kwallo a wasan sada zumunta.