Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Arsenal ya shiga sahun masu zawarcin tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho don ya maye gurbin kocinsa na yanzu Arsene Wenger a karshen kakar wasa ta bana.
Duk da yake rahotanni sun nuna Jose Mourinho ya tattauna da hukumomin kulob din Manchester United a asrice a kan yiwuwar horar da kulob din a karshen kakar wasa ta bana, kulob din Arsenal ya nuna bai cire rai a kan shawo kan Mourinho wajen komawa kulob din don cigaba da horarwa ba musamman a hasashen da ake yi na Arsene Wenger zai ajiye mukaminsa a karshen kakar wasa ta bana.
Shi dai kocin Arsenal, Arsene Wenger yana shan suka a wajen magoya bayan kulob din Arsenal tun bayan da kulob din FC Barcelona na Sifen ya fitar da shi a gasar cin kofin zakarun Turai (Champions League). Haka kuma kulob din Watford ya kara jefa na Arsenal cikin matsala bayan ya doke na Arsenal a matakin kwata-fainal a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA). Hakan ya bata wa magoya bayan kulob din rai, inda suka rika yin kira ga kocin ya sauka daga mukaminsa a karshen kakar wasa ta bana.
Tuni Arsene Wenger ya nuna fushinsa a kan kalaman magoya bayan kulob din, bayan sun nemi ya ajiye mukamin nasa.
Masana harkar kwallo suna ganin da wuya kocin bai yarda kwallon mangwaro don ya huta da kuda a karshen kakar wasa ta bana ba ganin yadda ya shafe kimanin shekara 18 yana kocin kulob din.
Yanzu dai lokaci ne kawai zai tabbatar da inda Mourinho zai koma don cigaba da horarwa.
Arsenal ta fara yunkurin maye Wenger da Mourinho
Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Arsenal ya shiga sahun masu zawarcin tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho don ya maye gurbin…