✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa Maso Yamma ta biya 1.81trn a matsayin kuɗin fansa a 2024 – Rahoto

Arewa Maso Yamma ta biya 'yan bindiga Naira tiriliyan 1.81 a matsayin kuɗin fansa a 2024.

Wani rahoto da Cibiyar Bincike ta Statisense ta wallafa, ya nuna cewar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ne a kan gaba wajen biyan ’yan bindiga kuɗin fansa a shekarar 2024.

Rahoton, ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2024, jimillar kuɗin fansar da aka biya a Arewa maso Yamma ya kai Naira tiriliyan 1.81.

Arewa ta Tsakiya ce, ta zo ta biyu, inda ta biya jimillar Naira biliyan 469.7.

Yankin Kudu maso Yamma, ya zo na uku da jimillar Naira biliyan 248.78, sannan Arewa maso Gabas ta ke da biliyan 166.14.

Sai kuma Kudu Maso Kudu da ya biya biliyan 90.05.

Kudu maso Gabas ne yanki na ƙarshe a wannan jerin, inda ya biya jimillar Naira biliyan 85.44.

Rahoton, ya kuma nuna cewa a shekarar 2024, jimillar kuɗin fansar da aka biya a Arewacin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 1.8, yayin da Kudancin Najeriya ya biya jimillar biliyan 424.27.

Hakazalika, rahoton ya bayyana cewa mafi yawan kuɗin fansar da aka biya sun fito ne daga ƙauyuka, inda aka biya jimillar tiriliyan 1.44.

A birane kuwa, an biya jimillar kuɗin fansa har Naira biliyan 794.46.