Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin zabubbukanta na mazabu da na kasa a wata sanarwar da ta aikewa hukumar zabe a ranar tara ga watan Afrilun shekarar 2018.
A wata wasika mai lamba: “APC/NHDQ/INEC/19/018/010” wacce aka yi wa lakabi da “Sanarwar Gudanar da Zabukan mazabu da na kasa” wacce Sakataren jam’iyyar na kasa, Mai Mala Buni ya sanya wa hannu ta nuna cewa zabukan mazabu za su gudana a ranar biyu ga watan Mayun shekarar 2018 na kananan hukumomi za a gudanar da shi a ranar biyar ga watan Mayun shekarar 2018, zaben jihohi zai gudana a ranar Laraba tara ga watan Mayun shekarar 2018 sai na kasa a ranar Litinin 14 ga watan Mayun shekarar 2018.
Sanarwar ta bayyana cewa “Mun rubuto don bayar da shawarar cewa jam’iyyar za ta gudanar da zabukan mazabu da na kananan hukumomi da na jihohi da kuma na kasa don cike guraban mukamai saboda nadin mukaman gwamnati ko mutuwa ko kuma wasu dalilai na daban kamar yadda kashi na 17 na kundin jam’iyyar ya tanada. Saboda haka muna sanar da ku cewa za mu yi zabe na musamman a kananan hukumomi don zaben wakilai da za su gudanar da babban zaben jam’iyyar . Saboda haka wannan sako na a matsayin sanarwa kamar yadda dokar zabe ta tanada”.