Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta shigar da kara a gaban Kotun Sauraron korafe-Korafen Zabe ta jihar tana kalubalantar zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Ahmed Aruwa ne ya sanar da haka ga manema labarai a Kano.
- ’Yan bindiga sun sace daliban jami’a mata biyu a Zamfara
- Dalilin da Shugaban NNPP na Kasa ya yi murabus
Ahmad Aruwa ya ce jam’iyyar ta shigar da korafinta ne tana karar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano.
Jam’iyyar ta APC ta ce sanar da sakamakon zaben da INEC ta yi ya saba da Dokar Zabe duba da cewa an tafka kura-kurai a cikinsa.
Tuni dai jam’iyyar ta shigar da korafin a gaban kotun wanda suka bai wa masana shari’a na jam’iyyar umarnin shigewa a gaba a shari’ar
Aminiya ta ruwaito cewa, dan takarar Gwamnan Kano na APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf murna bayan da INEC ta ba shi shaidar lashe zabe.