Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta iya lashe duk kujerun kananan hukumomin Jihar Gombe yayin zaben da za a gudanar nan ba da daɗewa ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafar cin abinci da ya shirya wa tsofaffin shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 11 da aka sauke bayan cikar wa’adin su a ranar 31 ga watan Disamba 2023.
- Sabuwar Shekara: Gwamnan Gombe ya yi wa fursunoni 39 afuwa
- Muhimman abubuwa daga jawabin Tinubu na Sabuwar Shekara
Ya bayyana cewa yana da yakinin jam’iyyar APC za ta iya lashe zaben idan aka gudanar da shi domin har kullum suna da goyon bayan al’umma, inda nan da wani lokaci gwamnatinsa za ta tsaida ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
“Zabe shi ne tushen mulkin dimokuraɗiyya don haka nan gaba kadan za mu sanar da ranar da za mu yi zaɓen ƙananan hukumominmu.”
A cewarsa, duk mai sha’awar tsayawa takara zai iya nema domin yana da ‘yancin tsayawa a matsayinsa na dan jiha.
Gwamnan yaba wa tsofaffin shugabannin riƙon ƙananan hukumomin bisa yadda suka yi wa jama’a da jihar su hidima, yana mai tabbatar da cewa har yanzu suna tare uwa ɗaya uba ɗaya.
Tun farko a jawabinsa na maraba, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Ci Gaban Al’umma Abdulkadir Muhammad Waziri, ya yaba wa tsofaffin shugabannin riƙon bisa kwazon da suka nuna.
Shi ma a jawabin sa na godiya a madadin tsofaffin shugabannin riƙon na ƙananan hukumomi, tsohon shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Akko, Abubakar Usman Barambu, ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa ba su damar yi wa al’umma hidima a wannan matsayi.