Jam’iyyar APC mai mulki ta ce bukatar da jam’iyyun hamayya suke gabatarwa ta soke Babban Zabe ba za ta taba yiwuwa ba.
APC ta bayyana haka ne a matsayin martani ga taron manema labarai da manyan jam’iyyun hamayya suka gudanar suna masu neman yanke kauna da Hukumar Zabe ta Kasa INEC.
- Jam’iyyun adawa sun bukaci a sake gudanar da sabon zabe
- PDP ta kwace duk kujerun sanatocin APC a Kaduna
Sa’o’i kadan da suka gabata ne jam’iyyun adawa uku — PDP da LP da kuma ADC — suka nemi soke zaben na ranar Asabar tare da bukatar tube Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa.
Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben na APC, Festus Keyamo, ya ce Shugaban Hukumar Zaben ta INEC zai saba doka idan har ya soke zaben da tuni ya riga ya fara bayyana sakamakonsa.
Mista Keyamo ya ce, “bukatar ba mai yiwuwa ba ce bisa doka. Suna gabatar da bukatar da ta saba doka.”
Ya ce mafita daya ce kawai ga ’yan hamayyar a yanzu, ita ce su je kotu idan ba su amince da sakamakon zaben ba.