A ranar Asabar da ta gabata ne APC ta kaddamar da Dakta Abdulmalik M. Durunguwa a matsayin dan takarar da zai wakilci kananan hukumomin Kachiya da Kagarko da ke kudancin jihar Kaduna a majalisar wakilai ta tarayya. Lokacin da yake jawabi bayan kaddamar da shi, Abdulmalik Durunguwa, ya nuna farin cikinsa, inda ya bayyana shugabanci ko wakilci a matsayin amana kuma a shirye yake da ya dauka domin kai jama’ar kananan hukumomin tudun mun tsira.
Durunguwa, wanda ya yi alkawarin tafiya tare tsakanin musulmi da kirista da adalci, ya kara bayyana cewa kananan hukumomin Kachia da Kagarko na da abubuwa guda biyu wadanda in har aka mayar da hankali a kan su za su iya bunkasa yankin da kuma jihar baki daya. Sannan ya sha alwashin yin matukar kokari wajen bunkasa harkokin noma da Allah ya albarkaci yankin da shi da kuma mayar da magudanar ruwa zuwa Dam din da za a iya amfani da shi wajen samar da wutar lantarki da inganta noman rani baya ga samun tsaftataccen ruwan sha da jama’ar yankin ke karancinsa.
Tunda farko a cikin jawabinsa, shugaban APC na jihar Kaduna, Hon. Shu’aibu Idris Maude wanda Hon. Yakubu Yatai ya wakilta, ya bayyana Durunguwa a matsayin dan takara mai inganci kuma wanda aka yi gwagwarmaya da shi tun farkon kafa APC, sannan ya yi kira ga jama’ar yankin da su yi watsi da maganar siyasar addini da na kabilanci don samun ci gaban da ya dace. Sannan dan takarar ya yi alkawarin baiwa marada kunya.
Haka shi shugaban matasa na ‘APC National Youth banguard’ da ke sa ido da kuma tabbatar da wanzuwar dimokradiyyar cikin jam’iyya, Mista Paul Aliyu, ya ce Durunguwa mutum ne nagartacce wanda ba ya nuna bambamci ko son kai tsakanin musulmi da kirista. Shi ko Kanar A.A Ladan (ritaya) kira ya yi ga wakilan da ke zabo ‘yan takara (Delegates) da su daina fuska biyu su tsaya su rika zabo nagartattun mutane.