Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a sanya watan Fabrairun shekarar 2022 a matsayin lokacin gudanar da babban taro tare da zaben shugabannin jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamnan Jihar Kebbi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Atiku Bagudu ne ya sanar da hakan, jim kadan da kammala wata ganawar sirri tsakaninsa da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Litinin.
Taron dai ya samu halartar Shugaban riko na jam’iyyar, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da kuma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar.
Bagudu ya ce an zabi watan na Fabrairu ne domin a ba ragowar Jihohi hudu da ba su samu gudanar da nasu zaben ba su yi hakan, sannan a kammala shagulgulan watan Disamba.
Shi ma da yake nasa tsokacin, Gwamna Mai Mala ya ce sai dai watan kawai aka tsayar, amma ba a tsayar da rana ba.
Ya ce za a sanar da ranar ne a nan gaba bayana sun aike da bukatar hakan ga Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) sannan sun kuma sun tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar.