Kwamitin riko na Jami’yyar APC karkashin Gwamna Mai Mala Buni ya bukaci a kori shugaban bangaren Sanata Kabiru Marafa a Jihar Zamfara, Alhaji Sirajo Garba daga jam’iyyar.
Hakan na dauke ne a wasikar da aka aiko wa Shugaban Jam’iyyar reshen Jihar Zamfara ranar 26 ga watan Agusta, 2020, mai dauke da sa hannun Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata John J. Akpanudoedehe
Wasikar ta zargi Alhaji Sirajo Garba kin yin biyayya ga umurnin shugabannin uwar jam’yya, wadanda a ranar 25 ga watan Yuni suka zartar cewar kada wani dan jam’iyyar ya shigar da kara kotu.
Sun kuma umarci wadanda suka shigar da karar su janye domin bai wa kwamitin rikon damar yin sulhu a cikin gida.
Shugabannin jam’iyyar sun koka a cikin wasikar cewar duk da umarnin da wasu matakai da ta dauka na bin umarnin ba a janye wasu kararraki ba.
Ya ce wasu ‘yan jam’iyya sun shiga da karar neman a rushe kwamitin riko da zababbun shugabannin jihohi na kalubalantar umarnin da shugabannin jam’iyyar suka baya.
“Kwamitin riko ya ba da umarnin shugabannin jam’iyya a jihohi su gaggauta yin kwamitin hukunci da zai fara shirye-shiryen korar Alhaji Sirajo Garba daga Jam’iyyar.
“Ana kuma jiran ku turo wa uwar jam’iyya duk wani hukunci da kuka yanke wa Alhaji Sirajo Garba, na bijire wa umarnin shugabannin jam’iyya.
“Yana kuma da kyau duk hukunci da kuka dauka ya zamto an ba shi damar kare kansa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya ce”, inji wasikar.
Haka kuma an ce, jam’iyyar a matakin jihar ta nada kwamitin da ya zauna ranar Talata kan bijirewar da bangaren Marafa ya yi, kamar yadda sakataren kwamitin, Barista Bello Umar Gusau ya shaida wa Aminiya.
Gusau ya ce har yanzu ba a kai ga daukar mataki kan ‘yan jam’iyyar 140 ba.
Ya kuma ce sun yi shelar zaman kwamitin a kan lamarin kuma sun sanar da ofisoshin jam’iyyar a matakan kananan hukumami.
- Ba a kore mu daga Jam’iyyar APC
A martanin da ‘yan bangaren Sanata Kabiru Marafa suka bayar, Sakataren watsa labarai, Alhaji Bello Bakyasuwa, ya ce har yanzu ba a turo musu wani mataki da jam’iyyar ta dauka kan su ba.
Bakyasuwa ya ce: “A yanzu haka ina cikin hedikwatar uwar jam’iyya a Abuja domin tabbatar da sahihancin wasikar da ta ce an kore mu kamar yadda abun ke yawo a kafafen sadarwa na zamani.
“Idan kana magana ne kan umarnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewar wadanda suka kai kara kotu su janye to ai mu tun kafin ya yi maganar muke shari’a.
“Mun ga wasikar a kafafen sada zumunta amma har yanzu ba a kira mu ba kuma ba a damka mana wasikar ba.
“Don haka, a gare mu, wasikar ba ta kai darajar takardar kumshe kosai ba.
“Kuma ko da gaskiya ce, ya kamata a kira mu a yi mana bayani.
‘Saboda haka, har yanzu mu cikakkun ‘yan jam’iyya ne”, inji shi.