✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe zaben shugaban kasa a Ekiti

Jam'iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa da kuri'a 201,494 a Jihar Ekiti

Jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa da kuri’a 201,494 a Jihar Ekiti a yayin da PDP ke bi mata da 89,554, LP 11,397 sai kuma NNPP 264.

Baturen zaben INEC a Jihar Ekiti, Farfesa Lasisi, wanda shi ne Shugaban Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya, Ila Orangun, ne ya sanar da haka bayan turawan zaben kananan hukumomi 16 na jihar sun gabatar da sakamakonsu.

Ya bayyana cewa “Jihar Ekiti na da masu rajistar zabe 988,923, wadanda daga ciki aka tantance 315,058.

“An samu sahihan kuri’u 308,171 da lalatattu 6,301 daga cikin 314,470 da aka jefa.”

Jihar Ekiti dai ita dan jam’iyyar APC ne gwamna, Biodun Oyebanji.