Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ciyaman 27 da kansiloli 312 a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Borno, da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zabe na Jihar (BOSIEC), Alhaji Lawan Maina ne, ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar ranar Lahadi a Maiduguri.
- Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga a Kaduna
- Yadda aka sace magidanci a hanyar zuwa filin jirgi a Abuja
“Bayan gudanar da zaben a ranar Asabar, a yau mun samu sakamako daga kananan hukumomi 27 kamar yadda doka ta ba mu dama karkashin sashe na 10.
“A matsayina na shugaban hukumar zaben jihar, zan karanto sakamakon zaben kamar haka:
“Jam’iyya mai mulki, APC ta lashe dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomin jihar 27.
“Kazalika, jam’iyyar ta lashe dukkanin kujerun kansiloli 312 a daukacin kananan hukumomin jihar.
“Da wannan, muka kawo karshen wannan zabe kuma za a gabatar da takardar shaidar lashe zabe ga wadanda suka yi nasara,” in ji Maina.