✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Dokoki a Bauchi

Dan takarar jam’iyyar APC, Honorabul Bala Ali Lukshi, ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar na maye gurbin dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Karamar…

Dan takarar jam’iyyar APC, Honorabul Bala Ali Lukshi, ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar na maye gurbin dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Karamar Hukumar Dass.

Da yake bayyana sakamakon zaben, ranar Asabar a garin Dass, alkalin zaben, Farfesa Ahmed Mohammed, ya bayyana Ali Lukshi na jam’iyyar APC a matsayin zababben dan majalisar dokoki mai wakiltar Karamar Hukumar Dass.

Farfsa Ahmed na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ya sanar da Ali Lukshi a matsayin zababben dan majalisar saboda ya cika ka’idojin da doka ta tanada na samun mafi yawan kuru’u a zaben da aka gudanar.

Ali Lukshi ya samu kuri’u 12,299 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Honarabul Lawal Bala Wundi da ya samu kuri’u 11,065.

Nasarar tasa ta biyo bayan kammala kada wa da kirga kuri’u a zaben da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar kan kujerar da ta bayyana babu kowa a kanta.