Jam’iyyar APC ta ce ta kai ƙarar Mai Shari’a Usman Na’abba na Babbar Kotun Jihar Kano gaban Hukumar da ke Kula da Harkokin Shari’a a Najeriya (NJC).
APC ta kai Alƙalin hukumar ne kan zargin neman tsoma baki a harkokin siyasa.
Hakazalika, jam’iyyar ta bayyana hukuncin a matsayin abin yin tir da watsi da shi.
A wata takarda da shugaban jam’iyyar mazabar Ganduje, mazabar da aka ce wasu shugabanninta biyu — Haladu Gwanjo da wani Laminu Sani — sun dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dokta Abdullahi Umar Ganduje, suka aika wa hukumar.
A cikin ƙarar mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Afrilu da sa hannun shugaban mazabar Ganduje da wasu shugabanninta 26, jam’iyyar APC ta Kano ta yi kira ga NJC da ta tantance ko Mai Shari’ar ya bi ka’idoji da tsarin doka wurin yanke hukuncin.
Sun kuma bukaci a dubi yiwuwar tsoma baki a harkokin jam’iyyun siyasa wurin tabbatar da ikirarin da wasu daga mazabar suka yi.
Takardar ƙarar ta ƙara da cewa: “Mu ‘yan kwamitin zartarwa na mazabar Ganduje ta Karamar Hukumar Dawakin-Tofa ta Jihar Kano, mun rubuto muku takardar nan ce domin kawo muku rahoto a hukumance tare da neman ku sa baki dangane da shari’ar da Mai shari’a Usman Mallam Na’Abba ya yi na jagorancin babbar kotun ta 4 a Jihar Kano, a wani hukunci da ya shafi jam’iyyar mu ta APC.
“Mai Shari’a Usman Mallam Na’Abba ya bayar da umarnin dakatar da Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan jam’iyyar APC ya kuma hana shi gudanar da aikinsa na shugaban jam’iyyar na kasa.”
Jam’iyyar ta ce ba a kai wa Ganduje sammaci ba, ta kuma ayyana yanke hukuncin da Mai Shari’a Na’Abba ya yi a matsayin shiga sha’anin jam’iyya wanda hakan sabawa doka ne.
“Wannan matakin ya kafa tarihi mai muni game da nuna son kai da kuma sa baki a harkokin gudanar da jam’iyyun siyasa.
“Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, muna kira ga hukumar da ke sa ido kan harkokin shari’a ta kasa: ta gudanar da cikakken nazari kan abin da ya faru, da hukuncin da Mai shari’a Usman Mallam Na’abba ya yanke na bayar da irin wannan umarni ga Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
“Muna fata NJC za ta dubi yiwuwar ɗaukar matakin ladabtarwa ga Mai Shari’a Usman Malam Na’Abba idan ta tabbatar da cewa ya yi abin da ya wuce ikonsa ko kuma ya yi wani abu da bai dace a ce jami’in shari’a ne ya aikata ba.”
Hakazalika, mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Farfesa Abdulkareem Kana, ya bayyana matsayarsu dangane da wannan batu.
Ya ce, jam’iyya mai mulki ba za ta mutunta ko kuma ta bi umurnin kotu ba, domin ya sabawa doka.
Kana ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi ga manema labarai a ranar Laraba da ta gabata.
Kana ya ce, Alƙali Na’Abba ya gudanar da haramtaccen hukunci, musamman in an yi la’akari da cewa bai aika wa Jam’iyyar APC ko Ganduje sammacin kotu ba, kawai ya yanke hukunci tashi guda.
Ya ce, “Dukkanmu mun ga ziyarar da shugabannin jam’iyyar mazabar Ganduje suka kai wa shugaban jam’iyyar a yau. Su ne mutanen da ya dace in ma za a shiga batun dakatarwa ne to su ne, amma kun ga yadda suka barranta kansu daga wannan ɗanyen aiki.
“Muna da labarin cewa wasu mutane sun dakatar da Dokta Abdullahi Umar Ganduje.
“Mun kai kararsu ga ’yan sanda kuma mun aika wa shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya kwafin abin da aka yi.
“Mun buƙaci su binciki mutanen da ke da hannu a ciki, musamman yadda duk manyan masu ruwa da tsaki a mazabar suka nesanta kansu daga matakin.
“Ba iya nisanta kansu daga matakin kaɗai suka yi ba, sun musanta duk wani abu da ya shafi dakatar da Dokta Ganduje.
“Ba mu san daga ina waɗannan abubuwa suke fitowa ba. Bincikenmu na farko ya nuna cewa zamba ne kuma wani abu ne mai kama da 419 ko damfara da wasu ke yi.
“Akwai wuce gona da iri wurin kirkirar takardun bogi da kuma yada su. Mu dai ba a bamu wata takarda ba.
An dai hango Ganduje yana magana da harshen Hausa a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafar intanet.
Ya yi wannan jawabi ne ga jiga-jigan jam’iyyar APC na mazabarsa da suka kai masa ziyarar nuna goyon baya.
Da yake jawabi ga shugabannin mazabar da suka ziyarce shi, Ganduje ya ce, “A jiya na je na ga mai girma shugaban kasa, na bayyana masa cewa abin da ya faru wasan kwaikwayo ne aka gudanar kuma ya amince.
“Shugaban kasa ya yaba muku, ya kuma ce in fada muku ku yi hakuri, ya kuma ba da tabbacin cewa har yanzu ni ne Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.”
Wannan dambarwa da ta kunno kai ta tada kura a fagen siyasar Najeriya, musamman ganin yadda aka gudanar da shari’ar dakatar da shugaban jam’iyyar APC a gaggauce.