A ranar Asabar Jam’iyyar APC mai mulki, za ta fara aikin tantance masu neman takarar kujerar gwamna da Majalisar Dokoki ta kasa a karkashinta.
Jam’iyyar ta ce za a fara aikin tantacewar ne jim kadan bayan taron kaddamar da shugabanni da sakatarorin kwamitin tantance masu neman takarar Majalisar Wakilai, Majalisar Dattijai da kuma kujerar gwamna.
- Batanci: Deborah ta wuce gona da iri, kada a zargi wadanda suka kashe ta —Farfesa Maqari
- Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu
Sakataren jam’iyyar na kasa, Sulaiman Argungu, ya sanar a safiyar Asabar cewa za a yi taron kaddamarwar ne da misalin karfe 12 na rana a otal din Fraser Suites da ke Abuja.
Argungu, ya ce daga bayan taron ne za a tantance masu neman takarar Majalisar Wakilai a ranar Asabar din, 14 ga watan Mayu, 2022, a otal din Zeus Paradise da ke Abuja daga karfe 2 na rana.
A ranar Lahadi 15 ga Mayu, 2022 kuma, za a gudanar da tantance masu neman takarar kujerar Sanata da masu neman kujerar gwamna a otal Fraser Suites, daga karfe 10 na safe.