✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya na farin ciki da kai saboda cire tallafin mai – APC ga Tinubu

Jam'iyyar APC ta jinjinawa shugaba Tinubu kan wasu matakai da gwamnatinsa ta zartar.

Shugabannin jam’iyyar APC sun shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa ’yan Najeriya sun yi na’am da irin matakan da yake dauka, musamman kan cire tallafin man fetur. 

Tinubu dai ya cire tallafin man fetur, wanda hakan ya sa ’yan Najeriya da dama suka koka da yadda ake fama da wahalhalu sakamakon tashin farashin man fetur, amma Shugaban ya tabbatar wa da jama’a cewa wahalar ta wucin gadi ce.

Da yake jawabi a ranar Alhamis a taron Majalisar Zartarwar jam’iyyar APC na kasa karo na 12, inda tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Sanata Basiru Ajibola suka zama sabon Shugaba da kuma Sakataren jam’iyyar na kasa, mukaddashin Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari, ya yaba wa matakin da Tinubu ya dauka.

“Jama’a na farin ciki da jajircewarku,” in ji Kyari.

Kyari, wanda aka nada a matsayin shugaban rikon kwarya a kwanakin baya, ya taya Shugaban Kasa da Mataimakinsa da daukacin zababbun ‘yan jam’iyyar murnar nasarar da suka samu, inda ya bayyana zaben Tinubun da aka yi a matsayin shugaban ECOWAS a matsayin nasara a siyasar kasashen waje ga Najeriya.

Ya yi alkawarin cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa tare da Shugaba Tinubu, “duk da kalubalen da ke gabanta.”

Ya ce jam’iyya mai mulki tana sane da sabbin kalubalen da ke gabanta a matsayinta na jam’iyya mai rinjaye a matakin Kananan Hukumomi, Jihohi da kuma Majalisar Dokoki ta Kasa.

Da yake jinjina wa wadanda suka kafa jam’iyyar, Kyari, ya ce jam’iyyar ta samu gagarumar nasara da kuma tagomshi daga ‘yan Najeriya tun bayan kafuwarta.

 Tun da farko a wajen taron, Tinubu ya jaddada bukatar biyan bukatun talakawa sakamakon cire tallafin da aka yi.

Shugaba Tinubu, ya jadadda biyan bukatun talakawa, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar APC, musamman sabbin shugabanni da su jajirce wajen tabbatar da shugabanci na gari wanda zai sake farfado da tattalin arziki da siyasar kasar nan.

Shugaban ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da cewa duk shirye-shiryen gwamnati za su amfanar tare da daukaka talakawan kasar nan maimakon jefa su cikin wahala.

Tinubu, wanda ya yi jawabi a taron NEC a karon farko tun bayan nasarar da ya samu a watan Fabrairu, ya jaddada cewa cin zabe mafarin samar da ci gaba ne. Ya ce gudanar da mulki da rikon amana wani kalubale ne na daban da ke bukatar ci gaba da kokari.

“Muna kan shirin kafa cikakkiyar gwamnati ta jama’a. A lokacina ne aka cire tallafin ,an fetur, kuma a yanzu ya rage mana mu biya bukatun talakawa cikin wani babban tsarin tattalin arziki da aka gyara,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su tabbatar da hadin kai, kwanciyar hankali, zumunci a tsakaninsu, don raya jam’iyyar tun daga tushe. Shugaba Tinubu ya kuma yi kira ga ‘ya’yan kam’iyyar da su mayar da hankali kan ci gaban kasa.

Dangane da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Fabrairu, ya kare sahihancin zaben. “Mun yi aiki tukuru, kuma mun karbi sakamakon. Cin zabe shi ne kashi na farko na tsarin. Abin da ke gaba shi ne shugabanci nagari da samar da ayyuka masu inganci. Dole ne mu samar da hadin kai, zaman lafiya da soyayya a jam’iyyar APC.

 “Kamar yadda nake fada a ko da yaushe, wadanda ba su amincewa da sakamakon zabe na gaskiya ba, ba su cancanci farin cikin samun nasara ba,” in ji shi.