✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya hana ni zuwa taron da aka tabbatar da Ganduje a Shugabancin APC — Buhari

Buhari ya bayyana cewar alkawarin da ya yi a baya ne ya yana shi halartar taron.

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na kasa ba a Abuja.

A yayin taron ne dai aka zabi tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar na riko na kasa.

Aminiya ta rawaito cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranakun 2 da 3 ga watan Agusta domin gudanar da tarukan kusoshin jam’iyyar na kasa da na kwamitin zartarwa na kasa (NEC).

Taron na kasa ya gudana ne a Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba, amma taron NEC ya tara shugabannin jam’iyyar a otal din Transcorp Hilton, ranar Alhamis.

Da yake bayyana dalilin da ya sa ya bai halarci tarukan ba, Buhari ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya ce bai je taron ba saboda alkawuran da ya dauka tun da farko.

Sanarwar ta ce, “Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin halartar taron jam’iyyar da kuma kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar APC, wanda aka gayyace shi.

“Ya mika uzurinsa, wanda ke nuni da cewa ba zai iya zuwa ba saboda alkawuran da aka yi a baya.

“Tsohon Shugaban Kasar ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana goyon bayansa da jajircewarsa ga jam’iyyar, tare da yi mata fatan samun hadin kai, yayin da shugabannin ke daukar matsaya kan batutuwa masu muhimmanci ga jam’iyyar da kasa baki daya.

Idan za a iya tunawa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shi ma ya nemi afuwar rashin zuwansa wajen taron, inda ya ce ya tafi halartar wasu taruka a kasar waje.

A ranar 17 ga watan Yuli ne jam’iyyar APC ta sanar da dakatar da taron jiga-jigan jam’iyyar na kasa baki daya.

Abubakar Kyari, mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi magana bayan taron gaggawa.

Taron wanda ya gudana a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, an kira shi ne bayan murabus din Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da kuma sakataren jam’iyyar na kasa, baki daya.

Kyari ya ce canjin shugabancin jam’iyyar ne ya sa aka dage taron.

Buhari ya taka rawar gani wajen zabar Sanata Abdullahi Adamu.

Kazalika, jam’iyyar APC ta ayyana tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan goyon baya da tsohon gwamnan ya samu daga shugaba Tinubu.