✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya tura su Abdulsalami domin tattaunawa da gwamnatin sojojin Nijar

Tinubu ya bukaci su su magance rikicin cikin ruwan sanyi

Shugaban ECOWAS, kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya aike da wata kwakkwarar tawaga domin tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin kwana bakwai da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ba sojojin su dawo da hambararren Shugaban Kasa, Mohammed Bazoum, ko ta afka musu.

A cikin wata sanarwa ranar Alhamis, Kakakin Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelele, ya ce matsayin na Tinubu ya zo daidai da abin da taron kungiyar na karshen makon da ya gabata a Abuja ya cim ma.

Tawagar dai wacce ke karkashin jagorancin tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta tafi birnin Yamai bayan kammala tattaunawa da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

A cikin tawagar kuma har da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da kuma Shugaban kungiyar ECOWAS Omar Alieu Touray.

Kazalika, Shugaba Tinubu ya aike da wata tawagar ta daban karkashin jagorancin Babagana Kingibe domin tattaunawa da shugabannin kasashen Libya da Aljeriya a kan rikicin na Nijar.

Shugaba Tinubu dai ya bukaci tawagar da ta yi aiki tukuru wajen ganin sun magance rikicin siyasar kasar cikin ruwan sanyi.

A makon da ya gabata ne dai sojojin suka yi juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum.