Kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC ya sanar da dage fara kamfen dinsa ranar Laraba zuwa sai abin da hali ya yi.
A ranar Litinin ce dai Kakakin kwamitin, Bayo Onanuga, ya ce za su bude yakin neman zaben da addu’o’i na musamman da kuma tattakin zaman lafiya a Abuja.
- Fiye da kaso 70 na Katsinawa na fama da matsanancin talauci – MDD
- Shugaban Kungiyar Malaman Musulunci ta Duniya ya rasu
To sai dai a wata sabuwar sanarwa ranar Talata a Abuja, Shugaban kwamitin, kuma Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce an dage farawar don a shigar da wasu karin jiga-jigan jam’iyyar.
Sanarwar ta ce, “Sakamakon fadada kwamitin don shigo da dukkan masu ruwa da tsaki da za su taimaka wa jam’iyyarmu, mun yanke shawarar kara lokacin saboda mu tabbatar duk wanda aka saka a ciki ya shirya.
“Saboda haka, shirye-shiryen da aka tsara farawa ranar 28 ga watan Satumba yanzu ba za su yiwu ba.
“A matsayinmu na jam’iyya mai mulki kuma mai farin jini a Najeriya, mun fahimci irin gudunmawar da mutane zai su bayar a tafiyar ga harkar takararmu.
“Za mu sanar da sabuwar rana da kuma abubuwan da za a yi nan ba da jimawa ba.”