✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC Na Kokarin Mayar Da Najeriya Siyasar Jam’iyya Daya —Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam'yyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar ya ce idan ba a yi da gaske ba Najeriya za…

Dan takarar shugaban kasa a jam’yyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar ya ce idan ba a yi da gaske ba Najeriya za ta koma tsarin siyasar jam’iyya daya.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakwancin kwamitin zartarwa na kungiyar jam’iyyun siyasar kasar nan (IPAC) ranar Talata a Abuja.

Ya bukaci jam’iyyun adawa na cikin kungiyar da su dage wajen farfado da ruhin dimokuradiyya a Najeiriya.

” Kun kawo mun ziyara ne saboda mu hada kai wajen dorewar dimokuradiyya, amma magana ta gaskiya siyasar mu tana neman komawa siyasar jam’iyya daya.

“Kuma kun san idan aka koma siyasar jam’iyya guda, to babu demukuradiyya,” in ji Atiku.

Ya bukaci jam’iyyun adawa na cikin kungiyar da su hada kai, domin kafa gamayya mai karfi da za ta kawar da jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Ya kuma zargi hukumar zabe ta kasa, INEC, da gudanar da zabe mai cike da kura-kurai da ba a taba ganin irinsa ba, inda ya ce “ku duba yadda INEC ta gudanar da zaben jihohi uku a kwanan nan, inda a Jihar Kogi ta sanar da sakamako da ke nuna kuri’un da aka kada sun fi yawan wadanda aka tantance a wata karamar hukuma.

“Ba za mu taba samun ingantacciyar dimokuradiyya ba, idan har INEC aikin ta shine faranta wa jam’iyya mai mulki.

“INEC ba za ta dawo da martabarta ba har sai an koma tsarin amfani da na’ura wajen kada kuri’a”.

Yabagi Sani shi ne shugaban kungiyar jam’iyyun siyasa na kasa, ya ce sun kai wa Atiku Abubakar ziyara ne saboda sun san shi da son dorewar mulkin dimokuradiyya.

Ya ce duk da matsaloli da ake fuskanta a lokutan zabe, mulkin dimokuradiyya shi ne mafi kyau a tsarin mulki.