✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC da PDP na cacar baki kan yunkurin dage zaben Edo

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP da ta APC mai mulki sun fara yakin cacar baki kan zargin yinkurin dage zaben gwamnan jihar Edo. Tuni dai…

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP da ta APC mai mulki sun fara yakin cacar baki kan zargin yinkurin dage zaben gwamnan jihar Edo.

Tuni dai jam’iyyun suka dukufa yakin neman zabe, yayin da ranar da aka tsara gudanar da zaben ta 19 ga watan Satumba ke kara matsowa.

A yayin wani taron manema labarai ranar Laraba a Abuja, Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Prince Uche Secondus ya zargi APC da matsa lamba ga Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta dage zaben.

“Bincikenmu ya gano cewa a mabambantan lokuta APC ta yi ta matsa lamba a kokarinta na jawo hankalin INEC ta dage zaben domin ta cimma mummunan kullin da take yi.

“Wannan ya saba wa tsarin dimokradiyya kuma yinkuri ne na kawo tarnaki ga zaben da sun san ba za su yi nasara ba.

“Muna sane da duk irin kulle-kullen da ake yi, ciki har da shigo da tsohon shugaban jam’iyyar Fadar Shugaban Kasa ta bayan fage domin tsara yadda za a murde zaben.

“A kan haka muke kira ga INEC da bangaren shari’a da su tashi tsaye wajen kare dimokradiyya kuma kada su sake su bayar da kai bori ya hau ga makarkashiyar APC,” inji Secondus.

– ‘Sokiburutuse kawai PDP ke yi’

To sai dai a martaninsa, Mataimakin Sakataren Watsa Labaran APC na Kasa, Yekini Nabena ya musanta zarge-zargen.

Ya ce, “A bayyane yake PDP ba ta shiryawa zaben jihohin Edo da Ondo ba, wanda kan haka ne ta bige da sokiburutsu.

“INEC hukuma ce mai zaman kanta, APC kuma jam’iyyar siyasa ce, saboda haka ba ta da hurumin da za ta iya magana a kan dage zaben.

“Mu a jam’iyyance, muna da kwarin gwiwar ko yau aka shiga zabe za mu lashe shi saboda irin abubuwan alheran da jam’iyyarmu ta yi a jihohin na Edo da Ondo.

“Babbar damuwarmu a yanzu ita ce yinkurin PDP na tayar da zaune tsaye lokacin zaben kamar yadda rahoton kungiyar Amnesty International ya hasashe.

“PDP ba ta da abin da za ta yi yakin neman zabe da shi, shi ya sa ta bige da kame-kame,” inji APC.

Zaben Gwamnan Jihar Edo na daukar hankalin kasancewar za a yi zazzafar fafatawa tsakanin gwamna mai ci, Godwin Obaseki da ya koma PDP da kuma Osagie Ize-Iyamu da ya ke yi wa APC takara kuma yake samun goyon bayan tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole.